Bugu da kari, Ban Ki-moon ya ce ya kamata a samarwa wadanda suke da bukatu karin kayayyakin kariya daga cutar ta Maleriya, da kuma koyar da jama'a karin fasahohin magance yaduwar sauro. A cewar sa wadannan ayyuka na bukatar karin kudade daga gamayyar kasa da kasa, ta yadda za a iya taimakawa kasashe mafiya fama da talauci kyautata tsarin kiwon lafiyar su yadda ya kamata.
Jiya Asabar ne dai ranar cutar Maleriya ta duniya, a kuma wannan rana ne Mr. Ban ya bayyana irin ci gaban da aka samu a aikin rigakafi, da na hana yaduwar ciwon na Maleriya tsakanin kasashen duniya.
Wani rahoton hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ya nuna cewa, tun daga shekarar 2000 ya zuwa yanzu, adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro ya ragu da kimanin kaso 50 bisa dari.
Rahoton ya kara da cewa an samu wannan nasara ne sakamakon kwarewa da aka nuna a bincike game da cutar zazzabin cizon sauro, da kuma amfani da fasahohin jinya masu nagarta, haka kuma a yanzu haka an kara samar da kayayyakin kandagarki masu amfani kwarai da gaske. (Maryam)