Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da ragowar zabukan ne a jihohin Abia, Imo, Taraba, da Delta da kuma jihar Kogi.
An ce cincirindon jama'a sun cika rumfunan zaben na jiya Asabar a jihar Taraba, wadda ke Arewa maso Gabashin kasar. Inda aka kada kuri'u a rumfuna 218 dake kananan hukumomin jihar 10. Yayin da kuma jami'an tsaro ke sanya ido a dukkanin wuraren da zaben ya gudana, domin kaucewa aukuwar tashin hankali.
A dai jihar ta Taraba, rundunar 'yan sanda ta kafa dokar hana zirga-zirga tun daga karfe 8 na safe zuwa karfe 5 na yammacin ranar ta Asabar, a wani mataki na tabbatar da tsaro a ranar zaben.
A daya hannun kuma INEC ta bukaci 'yan sanda da su dakatar da zirga-zirgar 'yan siyasa, da jami'an gwamnati, duka dai da nufin kammala zaben cikin kyakyawan yanayi. (Saminu Hassan)