in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga kasashen Afirka da su kara kwazo wajen murkushe zazzabin cizon sauro
2015-04-26 16:03:43 cri
Firaministan kasar Habasha Heilemariam Desalegn, ya bukaci mahukuntan kasashen dake nahiyar Afirka, da su kara kwazo wajen murkushe cutar zazzabin cizon sauro ko Maleriya daga nahiyar, duba da irin mummunan tasiri da cutar ke yi ga al'umma.

Firaministan na Habasha wanda ministan lafiyar kasarsa Kesetebirhan Admasu ya wakilta, a taron jagororin Afirka da aka gudanar a helkwatar kungiyar AU dake birnin Addis Ababan kasar ta Habasha, ya kara da cewa a wannan gaba da ake gudanar da bukukuwan ranar cutar Maleriya ta duniya, ya zama wajibi nahiyar Afirka ta tunatar da kan ta muhimmancin dake akwai, na kare rayuwan al'ummar ta daga salwanta sakamakon ci gaba da yaduwar wannan cuta.

Alkaluma dai sun nuna cewa nahiyar Afirka ce ke da kaso 82 bisa dari na masu kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro, kana 'ya'yan nahiyar ne ke da kaso 90 bisa dari, na yawan wadanda Maleriya ke hallakawa a dukkanin duniya.

Duk da nasarorin da aka samu game da yakin da ake yi da wannan cuta a sassan nahiyar daban daban musamman a baya bayan nan, a daya hannun mahalarta taron na jiya Asabar sun bayyana bukatar kara zage damtse, wajen kara fadada ayyukan da ake gudanarwa a wannan fanni. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China