in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin taya murnar cika shekaru 60 da kiran taron Bandung
2015-04-23 15:56:38 cri

Shugabannin kasashen Asiya da Afirka sun taru a birnin Jakarta, babban birnin kasar Indonesia a jiya Laraba 22 ga watan nan, don taya murnar cika shekaru 60 da kiran taron Bandung. Shugabannin kasashen Asiya da na Afirka, ciki hadda shugaban kasar Sin Xi Jinping sun hallara. Cikin jawabin sa shugaba Xi ya bayyana yadda a yanzu haka kasashe masu tasowa suke hada kai, da taka muhimmiyar rawa, da sa kaimi ga samun bunkasuwa cikin daidaito a duniya, kana ya yi alkawarin cewa, har abada Sin za ta kasance abokiya ta hakika ga kasashe masu tasowa.

A cikin shekaru 60 da suka gabata, nahiyoyin Asiya da Afirka sun canja daga yankuna masu talauci, zuwa yankuna mafiya samun damar bunkasuwa, kuma matsayinsu ya daga a fadin idanun mutanen duniya.

Yawan mutanen nahiyoyin biyu ya kai kashi uku cikin hudu na dukkan al'ummar duniya, kana yawan kasashe membobin MDD daga nahiyoyin biyu ya zarce rabin dukkan membobin MDDr, don haka hadin gwiwar Asiya da Afirka yana da babbar ma'ana ga dukkan duniya.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasashe masu tasowa suna da buri daya na gaggauta samun bunkasuwa, da kyautata zaman rayuwar jama'a, don haka ya kamata su hada kai da yin kokari tare. Banda batun hadin gwiwa a tsakanin kasashen Asiya da Afirka, ya kamata a kara hadin gwiwa a tsakanin kasashen da na Latin Amurka, da na yankin kudancin tekun Pasifik, da sauran yankunan duniya, ta haka za a kara karfin tabbatar da zaman lafiya a duniya, tare da sa kaimi ga samun bunkasuwa tare.

Game da hakan mataimakin shugaban kwalejin nazarin batutuwan duniya na kasar Sin Ruan Zongze, ya bayyana cewa bisa bunkasuwar kasashe masu tasowa, kasashen Asiya da Afirka sun kara taka muhimmiyar rawa kan dangantakar dake tsakanin kasa da kasa. Shugaba Xi ya yi kira ga yada tunanin Bandung, da bayyana sabon ra'ayinsa game da tunanin, ya sa kaimi ga raya tsarin duniya da odar kasa da kasa mai adalci. Wannan ya bayyana cewa, a nan gaba, kamata ya yi kasashen Asiya da Afirka su kara taka muhimmiyar rawa a dandalin kasa da kasa.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, tunanin Bandung ya dace da hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, baya ga babbar ma'ana ga hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa da masu ci gaba da tunanin na Bandung yake da shi.

A ganin Ruan Zongze, kiran da aka yi kan hadin gwiwar tsakanin kasashe masu tasowa, da masu ci gaba, ya alamta ra'ayin Sin na bude kofa, da amincewa da bambance-bambancebancin ra'ayi. A lokacin da ake raya duniya bisa tsari na bai dayaneman dunkulewar tattalin arzikin duniya, banda hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, ya kuma kamata a kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa da masu ci gaba, ta haka za su iya tinkarar kalubale yadda ya kamata, tare da samun damar bunkasuwa tare.

Xi Jinping ya ce, ko da an samu babban canji a duniya ko a'a, kasar Sin za ta kasance abokiya ta hakika ga kasashe masu tasowa har abada. Wannan ne tushen manufofin harkokin waje na kasar Sin, ba kuma za a canja wannan yanayi ba har abada.

Shugaba Xi ya gabatar da wasu matakan sa kaimi ga hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Asiya da Afirka a cikin jawabin na sa. Kana ya bayyana cewa, kasar Sin na fatan ci gaba da kokari tare da bangarori daban daban, wajen gudanar da shirin "shirin zirin tattalin arziki na siliki da hanyar Siliki ta ruwa na karni na 21 Ziri daya da hanya daya", da raya bankin zuba jari ga ayyukan more rayuwa na Asiya wato AIIB, da kuma yin amfani da asusun hanyar siliki yadda ya kama.

A nashi bangaren, Ruan Zongze ya bayyana cewa, yawancin kasashen dake bin shirin "Ziri daya da hanya daya" ya shafa kasashe ne masu tasowa. Kuma Duk da cewa akwai kasashe masu ci gaba da suka shiga bankin na AIIB, amma yawancin membobin bankin kasashe masu tasowa ne. Wadannan shirye-shirye sun maida hankali ga hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, kuma kasashen masu tasowa ne za suda kuma sanya su kara samun moriya. Wannan ya bayyana cewa, Sin ta zama abar koyi yayin da ake raya hadin gwiwar dake tsakanin kasashe maso tasowa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China