in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da takwaransa na Zimbabwe
2015-04-23 15:09:18 cri

A yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Zimbabwe Robert Mugabe a birnin Jakarta.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 35 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Zimbabwe, kuma kasar Sin na da aniyar yin kokari tare da kasar Zimbabwe wajen ciyar da huldarsu gaba. Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da karfafa zukatan kamfanoni da hukumomin hada-hadar kudinta, wajen tattaunawa tare da bangaren Zimbabwe, a kokarin lalubo bakin zaren tattara kudade, ta yadda za ta ba da tallafi wajen raya muhimman ababen more rayuwa a kasar.

A nasa bangare, Robert Mugabe ya ce, kasar Zimbabwe na darajanta zumuncin gargajiya a tsakaninta da kasar Sin, tare da nuna godiya ga goyon bayan da Sin ke nuna mata, wajen tabbatar da mulkin kai da raya tattalin arziki.

Haka zalika, Mr. Xi ya jaddada cewa, kasar Sin za ta zurfafa aikin hadin gwiwa na aminci a tsakanin kasashen biyu, bisa damar shirya taron ministoci na 6, na dandalin tattaunawa a tsakanin Sin da kasashen Afrika, domin ciyar da sabuwar huldar abokantaka a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare.

Mr. Robert Mugabe ya nuna amincewa da kalaman shugaba Xi, ya kuma yi wa kasar Sin godiya, bisa babbar gundummawar da take baiwa kasar Zimbabwe.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China