in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya yanke kudurin rage yawan sojojin tawagar musamman na majalissar dake Laberiya
2015-04-03 14:46:46 cri
  

Kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri a jiya Alhamis, inda aka amince da rage sojoji 1501 daga tawagar musamman na majalissar dake Laberiya.

Kudurin ya ce, kwamitin sulhu na MDD ya yaba ma gwamnatin Laberiya game da yadda take tinkarar cutar Ebola, ya kuma ba da izni ga babban sakataren majalissar wajen rage yawan sojojin tawagar ta dake kasar a kai a kai.

A shekarar 2003, kwamitin sulhu ya kuduri niyyar tura tawagar musamman zuwa kasar Libiya, domin tallafawa wajen gudanar da yarjejeniyar tsagaita wuta, da kiyaye zaman lafiya, da kuma farfado da kasa bayan yaki. A shekarar 2012 kuma kwamitin ya yanke kudurin rage yawan sojojin tawagar bisa matakai 3.

A sakamakon yaduwar cutar Ebola a kasashen yammacin Afrika ciki har da kasar Laberiya, kwamitin sulhu na MDD ya jinkirtar da tattaunawa kan yin kwaskwarima ga tawagar musamman dake kasar. A watan Maris na wannan shekara, mataimakin sakataren MDD mai kula da aikin kiyaye zaman lafiya Herve Ladsou ya ba da rahoto ga kwamitin sulhun cewa, a lokacin da ake samun sassauci kan cutar Ebola, za a iya ci gaba da rage yawan sojojin tawagar majalisar ta la'akari da halin zaman lafiya da ake ciki a kasar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China