Masu gudanar da bikin sun bayyana cewa, domin sada zumunci, hukumar sada zumunci da kasashen waje ta Sin, da kwamitin kiwon lafiya da kayyade iyali na kasar, da hukumar kiwon lafiya ta babbar hukumar aikin ba da guzuri ta rundunar sojan kasar sun gudanar da wannan aiki mai suna "zabar fitattun likitocin Sin da suka ba da taimako a kasashen waje", da zummar mai da hankali kan rukunin likitoci dake aiki a ketare, a kokarin bayyana yadda suke samar da taimako ga marasa lafiya duk da matsalolin da suke fuskanta, da kuma yadda jama'ar kasar ke son zaman lafiya da darajanta rayuwa.(Fatima)