in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron majalissar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin
2015-03-13 20:00:20 cri

An kammala taron shekara shekara na majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin a yau Juma'a 13 ga wata a nan birnin Beijing.

Yayin taron, 'yan majalisar kimanin 2200 sun sauke nauyinsu na ba da shawarwari, da sa ido, da tsoma baki cikin harkokin siyasa, tare da gabatar da shawarwari fiye da 5800.

An ce, taron na wannan karo ya taimaka matuka wajen tabbatar da tsarin raya kasar Sin a fannoni hudu da aka gabatar, wadanda za a mai da su cikin littafin raya majalisar.

A taron da aka kammala, an zartas da kudurin rahoton ayyukan majalisar. A matsayin wani abin koyi a fannin ba da shawara a siyasance, 'yan majalisar fiye da dubu 2, sun tattauna da kuma ba da shawara kan harkokin kasar ta Sin. Haka kuma an tattara takardun jawabi 510, da na shawarwari 5857, kuma an gudanar da muhawara na rukuni rukuni har 12 cikin taro na tsawon kwanaki 10.

Mataimakin direkatan sashen kula da shawarwarin da aka gabatar na majalisar, Mr Ren Tianjie ya bayyana cewa, shawarwarin da aka gabatar sun shafi fannoni daban-daban, ciki hadda tsare-tsaren kasa, da na zaman rayuwar jama'a, da ma abubuwan da suke matukar jawo hankalin mambobin. Mr Ren ya ce:

"Shawarwarin da aka gabatar sun karkata matuka ga fannoni da dama, ciki hadda sabon yanayin da kasar Sin ke ciki wajen raya tattalin arziki, da kuma tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki cikin karko, da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar na 13, da kuma tsarin 'Ziri daya hanya daya', da tsarin raya biranen Beijing, da Tianjing da lardin Hebei, da raya yankunan da kogin Yantse ke malala."

Dadin dadawa, wasu abubuwan da suka jawo hankalin mambobin sun hadda da zurfafa yin kwaskwarima ta fuskar tsarin kasafin kudi, da na haraji, da hada-hadar kudi, da kyautata tsarin shari'a da dai sauransu. Baya ga haka kuma, akwai batun kira ga sa kaimi a fannonin ba da ilmi, da na samar da guraben aikin yi, da ba da kulawa ga tsoffi, da ingancin magunguna da kiwon lafiya, da kiyaye muhalli da dai sauran, batutuwan dake da matukar nasaba da zaman rayuwar jama'a.

Misali, Chi Fulin, wani dan majalisar a yayin taron ya gabatar da wasu batutuwa da ya kamata a maida hankali yayin da ake aiwatar da sauye-sauye a fannin bunkasa tattalin arziki, ya ce

"Dora muhimmanci kan sha'anin ba da hidima yayin da ake sauya hanyar samar da bunkasuwar tattalin arziki, mataki ne wanda baya ga haifar da bunkasuwar tattalin arziki bisa matsakacin sauri, zai kuma samar da amfani matuka wajen kara samar da guraben ayyukan yi, da ciyar da aikin kwaskwarima da ake yi a sauran fannoni gaba."

Ban da haka kuma, mambobin sun tofa albarkacin bakinsu kan wasu matsalolin da ake fuskanta, daya daga cikinsu ya ce,

"Tattara jari abu ne mai wuya, kuma ba a warware matsalar ba, gwamnatin ba ta samar da isassun ababen more rayuwa, baya ga karancin ayyukan bada hidima, da kuma nauyin biyan haraji da ake fuskanta."

Wadannan shawarwari dake kunshe da muradun jama'a sun bayyana muhimmin matsayin majalisar cikin ayyukan siyasa na kasar Sin. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China