Shugabar kasar Chili, Michelle Bachelet da sakatare janar na MDD Ban Ki-moon sun cimma rattaba hannu bayan kammala taron na kwanaki biyu kan wani kundi mai taken "Yin kira ga aiwatarwa"
Ana kira ga maza da mata da su gaggauta kawo sauye sauye domin kai ga cimma wannan buri na daidaici, ba wai cikin shekaru da dama masu zuwa ba amma cikin dan kankanin lokaci, in ji madam Michelle Bachelet a cikin wani jawabinta na rufe taron na manyan jami'ai kan "matan dake shugabanci da daukar matakai"
Zaman taron na da manufar bullo da hanyoyin gaggauta ci gaba kan maradun da aka tsai da a yayin babban taron duniya na mata karo na hudu, da aka shirya a shekarar 1995 a birnin Beijing na kasar Sin.
Mista Ban Ki-moon ya bayyana cewa duniya ba za ta cimma burinta ba dari bisa dari idan aka nuna wariya ga kashi 50 cikin 100 na al'ummarta, tare da kara bayyana cewa yanzu lokaci ya yi na daukar mataki domin cike wannan gibi, da fuskantar kalubale da kuma zuba jari ga mata da 'yan mata. (Maman Ada)