in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da farmakin da kungiyar Boko Haram ta kai wa fararen hula
2015-02-28 13:01:24 cri

A jiya Jumma'a, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya ba da sanarwa ta hannun kakakinsa, inda ya yi Allah wadai da jerin farmakin da kungiyar Boko Haram ta kai wa fararen hula dake kasashe daban daban, ya kuma yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su dakile wannan kungiya tare.

Sanarwar ta ce, Ban Ki-moon ya sake la'antar farmakin da kungiyar Boko haram ta kai wa mazaunan dake kasashen Kamaru da Chadi da Nijer da kuma Nijeriya, musamman ma yadda wannan kungiya take garkuwa da yara domin mayar da su zama 'yan kunar bakin wake abin da ya ce hakan, ba zai samu gafara daga jama'ar duniya ba.

Sannan kuma, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, ana maraba da ayyukan yaki da kungiyar Boko Haram da sojojin kasashe daban daban suke yi bisa jagorancin kungiyar tarayyar kasashen Afrika, don haka ya kamata kasashen duniya su goyi bayansu. Sai dai a sa'i daya kuma, ya kamata a gudanar da irin wannan aiki bisa dokar kasa da kasa.

Sanarwar ta kara da cewa, ban da daukar matakan soja kan kungiyar Boko Haram, ya kamata a dauki matakai iri iri domin kawo karshen rikicin, ta yadda za a iya rage barazanar da kungiyar ta yi wa mazaunan yankin.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China