in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karuwar yawan mutane na kalubalantar kasuwannin gidaje a Afrika
2015-02-27 14:26:28 cri

Wakilin bankin raya Afrika dake birnin Dakar Mamadou Lamine Ndongo, ya ce karuwar yawan mutane cikin sauri zai haifar da kalubale ga kasuwannin gidaje na wasu kasashen Afrika.

Ndongo ya bayyana hakan ne yayin wani taron kara wa juna sani game da raya kasuwar gidaje da gine-gine a Afrika, da aka gudanar a birnin Dakar na kasar Senegal a kwanan nan.

Mr. Ndongo ya ce cikin shekaru 10 da suka gabata, yawan al'ummar Afrika ya yi matukar karuwa, a ciki yawan karuwar mutane a birane ya kai kashi 3.5 cikin dari a ko wace shekara. Hakan ya sa yawan mazauna birane ya kai kimanin biliyan 1.1, yayin da ake kuma hasashen wannan adadi zai ninka sau daya nan da shekarar 2050.

Ana dai ganin saurin karuwar yawan mutanen nahiyar ta Afirka a matsayin matsalar dake kawo babban cikas ga batun mallakar muhalli, matakin da ya sanya al'ummar Afrikan kimanin miliyan 200 rayuwa ba tare da cikakken muhalli ba.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China