in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen gabashin Afirka na kokarin samar da wutar lantarki ta hanyar sarrafa shara
2015-02-26 16:41:11 cri

A birnin Kampala, fadar mulkin kasar Uganda, akwai wata babbar mahauta wadda ke samar da nama ga dukkan kasuwannin birnin, inda a kan yanka shanu 700, da awaki 200, da kaza 300 a ko wace rana. Amma aikin da ake yi a mahautar kan gamu da katsewa, sakamakon daukewar wutar lantarki a kai a kai. Don ci gaba da aikin, ma'aikata na ta da janareto, duk da cewa hakan na haifar da fitar iska mai gurbata muhalli, tare da kara yawan kudi da ake kashewa wajen gudanar da sana'a a mahautar.

A sa'i daya, mahautar tana fidda shara daga jinin dabbobi, da kayan ciki, da gurbataccen ruwa, zuwa cikin tabkin Victoria dake dab da ita, lamarin da yake tsananta gurbacewar muhalli, da barazana ga lafiyar jikin dimbin jama'a da ke zaune a kewayen wannan babban tabkin.

Mahautar ta kasance wani masali na yadda kasashen gabashin Afirka suke kokarin raya masana'antun da suka shafi aikin noma, sai dai a wani bangare kuma, karuwar shara da ake samu, daga dabbobin da ake yankawa, ita ma ta zama wata matsala ga kokarin kare muhalli. A sabili da haka ne, wasu kasashen dake gabashin Afirka suka kaddamar da ayyuka na samar da wutar lantarki bisa sarrafa wadannan abubuwan shara.

A karkashin wannan shiri ne, yanzu haka ake gudanar da wani gwaji a kasashen Uganda, Tanzania, da Habasha, wanda ya shafi mahautar ta birnin Kampala. Bisa gwajin da ake yi, an fara tara kayan cikin dabbobi, da jininsu da dai sauran tarkacen shara, sa'an nan a ruba ta don samar da iskar gas da a kan samar daga taki. Ta iskar gas din ne kuma ake samar da wutar lantarki, wadda za a samarwa mahautar don gudanar da aikinta.

A cewar mista Joseph Kyambadde, shugaban sashen kimiyyar harhada sinadarai na jami'ar Makerere ta kasar Uganda, wanda yake da hannu cikin wannan shiri na samar da wuta, bisa sarrafa abubuwan shara wadanda aka samu daga dabbobin da ake yankawa a mahautar, ana iya samar da iskar gas har cubic mita 10 zuwa 15 a ko wace rana. Kana bayan samun iskar da ta kai cubic mita 60, za a iya samar da isasshiyar wutar lantarki ga dukkan fitilu 15 na mahautar, da injin kankara guda 30. Ta haka za a samu damar tsimin kudin wuta da yawansa ya kai dala 2800 a ko wane wata. Har ila yau kuwa, kudin da a kan kashe don sayen man janareto shi ma zai ragu daga dala 1200 zuwa 105, adadin da ya yi kasa da kashi 90 da wani abu bisa dari.

Masu kula da wannan aiki na amfani da abubuwan shara don samar da wutar lantarki, suna da imani kan aikin da suke yi, ganin yadda suke shirin sayar da wutar lantarki ga gwamnati, bayan da yawan wutar da ake fatan samarwa ta isa a gudanar da dukkan ayyukan mahautar.

A nata bangare, kasar Kenya dake makwabtaka da Uganda, ita ma ta fara gwajin aikin samar da wutar lantarki da shara. Yanzu haka ana sa ran ganin wata ma'aikata mai taken Biojoule ta fara samar da wutar lantarki, da za ta kai Megawatt 2 ga hukumar kasar a watan Maris mai zuwa. An ce wutar da za a samar za ta biya bukatun iyalai kimanin 8000, idan an lasafta ta bisa wani matsakaicin matsayi na yin amfani da wutar lantarki ta al'ummar kasar Kenya.

Wannan ma'aikata mai fadin kadada 800, dake dab da tabkin Naivasha dake da tazarar kilomita 90 da wani abu da birnin Nairobi, tana amfani ne da rubabben ganyayen lambu, da karmamin masara, da sauran abubuwan shara, domin samar da iskar gas, wadda za a kona don samar da wutar lantarki. Ma'aikatar ta kasance irinta na farko a kasar Kenya, wadda za ta ba da gudunmawa ga tsarin samar da wutar lantarki a kasar.

Hakika kasashen gabashin Afirka suna ta kokari a shekarun baya-bayan nan domin samar da wutar lantarki bisa yin amfani da tsabtaccen makamashi, inda suke kafa, ko kuma kokarin kafa wasu tsare-tsare na samar da lantarki daga zafin kasa, ko karfin ruwa, ko iska, da dai sauransu.

Wadannan ayyukan sun sanya kasashen gabashin Afirka samun karin hanyoyin samar da wutar lantarki. Amma wannan fasaha ta yin amfani da shara wajen samar da wuta, ta dace a kara yayata ta, zuwa wurare daban daban na nahiyar ta Afirka, ganin fasahar tana da araha, baya ga saukin samar da abubuwan shara, da sauran ragowar sassan dabbobi a yankunan nahiyar.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China