in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi allahwadai da kisan 'dan kasar Jordan da IS ta yi
2015-02-04 10:21:29 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi allahwadai da kisan matukin jirgin saman nan 'dan kasar Jordan Moaz al-Kasasbeh da kungiyar IS ke garkuwa da shi ta yi.

Mr. Ban wanda ya bayyana hakan ta kafofin watsa labarai, ya bayyana kisan a matsayin rashin imani inda ya bayyana goyonsa ga bayan al'ummar kasar ta Jordan wajen yin allahwadai da wannan mummunan aiki na rashin tausayi ga bil-adama.

Bugu da kari Ban Ki-moon ya bukaci gwamnatoci da su kara kokarin da suke na yaki da ayyukan ta'addanci kamar yadda dokokin kare hakkin bil-adama suka tanada.

Bayan samun wannan labarin, shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya bayyana kudurin ganin bayan kungiyar. Kana ya bukaci kasashen duniya da su kara hada kai a kokarin da ake na ganin an kakkabe ayyukan kungiyar kwata-kwata.

Mayakan na IS sun kama al-Kasasbeh ne bayan da jirginsa ya fadi a kusa da birnin Raqqa na kasar Syria a watan Disamban shekarar da ta gabata, inda gwamnatin kasar Jordan ta bayyana kudurinta na yin musayarsa da 'dan jaridar nan 'dan kasar Japan Kenji Goto. Amma hakan bai yi nasara ba, sakamakon karewar wa'adin ranar 29 ga watan Janairu da Jordan din ta bukata na samun tabbaci daga IS cewa, 'dan kasar nata yana raye ko a'a.

A jiya Talata ne kungiyar ta IS ta fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna yadda aka kona matukin jirgin 'dan kasar Jordan da ransa a cikin wani keji. Wannan na zuwa ne kwanaki bayan da mayakan na IS suka fille kan 'dan jaridar nan 'dan kasar Japan

Yanzu dai kasar Jordan ta tabbatar da sahihancin bidiyon, kana ta lashi takwabin daukar fansa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China