in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Malaysia ta sanar da faduwar jirgin saman MH 370
2015-01-29 20:40:43 cri

A yau ne, hukumar kula da harkokin jiragen saman fasinjoji ta kasar Malaysia ta sanar da tabbatar da faduwar jirgin saman kasar mai lamba MH 370, kana tana ganin cewa, dukkan fasinjoji da ma'aikata su 239 da ke cikin jirgin sun rasa rayukansu.

Dangane da lamarin, Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, gwamnatin kasar Sin ta yi bacin rai matuka kan mutuwar fasinjojin da ma'aikatan jirgin, sa'an nan ta tausayawa iyalan mamatan tare da yi musu jaje.

Ta kara da cewa, bayan abkuwar hadarin jirgin, Malaysia ta yi kokari sosai wajen neman jirgin, bin bahasin hadarin da kwantar da hankalin iyalan fasinjojin da dai sauransu. Har wa yau kasar Australia da sauran kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sun nuna goyon baya da ba da taimako wajen neman jirgin da dai makamantansu. Kasar Sin ta yaba tare da nuna musu godiya da kokarin da suke yi. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China