in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha a fannin sadarwa sun tallafawa bunkasar ayyukan gona a Afirka
2015-01-29 16:19:36 cri

A 'yan kwanakin nan ne aka kaddamar da wani shafin intanet na ayyukan gona mai suna "An Invest Africa" a gabashin nahiyar Afirka, wanda ya hada da kididdiga ta iri daban daban, da suke da nasaba da ayyukan gona na kasashen da ke gabashi, da tsakiya, da kuma kudancin Afirka, a wani mataki na kokarin shimfida gada tsakanin manoma, da masu zuba jari, da masu sayen amfanin gona da ma masu tsara manufofi a fannin musayar labarai, ta yadda za a ba da taimako wajen bunkasa gudanar ayyukan gona. Hakan ya sa wannan shafin intanet ta zama wani sabon matakin da kasashen Afirka ke dauka, wajen sa kaimi ga ci gaban ayyukan gona bisa hanyar kirkiren kimiyya da fasaha.

Sanin kowa ne cewa, aikin gona ya kasance sana'a mafi muhimmanci ga akasarin kasashen Afirka, wanda jimillar GDP da yake samarwa ya kan kai sulusi, bisa na daukacin sana'o'in da al'ummar Afirka ke gudanarwa. Haka kuma yana baiwa mutanen da yawansa ya zarce kashi 60 cikin dari na nahiyar, damar samun guraban aikin yi. Don haka ana iya cewa, ci gaban ayyukan gona zai ba da gudummawa wajen magance matsaloli masu dimbin yawa, kamarsu rashin isasshen hatsi a Afirka, da matsalar ikon mallakar gonaki, da rikice-rikice a tsakanin kalibu daban daban, da karanci ko rashin samun guraban ayyukan yi, gami da talauci.

Alal hakika raya ayyukan gona yadda ya kamata, zai kasance tamkar wani mabudi ne na warware wadannan matsalolin da ke gaban miliyoyin al'ummar Afirka.

Domin gaggauta bunkasar ayyukan gona, da kuma kauda cikas ga ci gaban ayyukan gona, shugabannin kasashen Afirka sun daddale yarjejeniya dake kunshe cikin sanarwar Maputo a shekarar 2003 a kasar Mozambique, inda aka gabatar da cewa, kasashen Afirka za su kebe a kalla kashi 10 cikin dari na kasafin kudinsu a ko wace shekara, domin raya ayyukan gona, a kokarin cimma burin samun karuwar sha'anin noman da kashi 6 cikin dari.

Sai dai a cikin shekaru goma da suka gabata, ba a aiwatar da wannan yarjejeniya yadda ya kamata ba, amma duk da haka an samu wasu sakamako masu kyau, game da batun sa kaimi ga ci gaban ayyukan gona bisa amfani da fasahohin sadarwa wanda ya fi jawo hankalin mutane.

Alal misali, an fitar da wata manhajar tafi da gidanka da ake amfani da ita a cikin wayar salula mai suna ICow a kasar Kenya. Bayan da masu kiwon shanu suka yi rajista a cikin manhajar, to za su iya samun labarai kan adadin lokacin haihuwa na shannun su, da bayanai kan hanyoyin shawo kan cututtuka da dai sauransu ta cikin wayoyin salular su. Bugu da kari, za a iya yin amfani da wannan manhaja wajen duba farashin abincin da ake samarwa daga madara a kasuwa. Wannan manhaja ta yi matukar samun karbuwa wajen masu kiwon shanu na kasashen Kenya, da Uganda, da kuma Tanzania.

A cikin wadannan shekaru da suka gabata, manhajojin tafi da gidanka da ake amfani da su cikin wayar salula, da kasashen Afirka suka kirkira suna kokarin samar da hidimomi iri daban daban, ciki har da hasashen yanayin halittu, da nuna yawan kayayyakin gona da ake iya samar da farashinsu, da yin ciniki ta intanet, kana da more fasahohin ayyukan gona da dai sauransu.

A ciki, manhajojin da suka fi samun karbuwa akwai Esoko na kasar Ghana, da Agro-Hub na kasar Kamaru, da M-Farm da Kimilo da Salama na kasar Kenya.

Bisa rahoton da babban tsarin hada wayoyin sadarwa na duniya GSMA ya bayar, an ce, akwai cibiyoyin kirkire-kirkiren fasahar sadarwa fiye da 50 a nahiyar Afirka, ciki har da cibiyar Hive Colab ta kasar Uganda, da cibiyar Limbe Labs ta kasar Kamaru, da kuma iHub ta kasar Kenya, wadanda suke kokarin kirkiro manhajojin fasahohin sadarwa, bisa goyon bayan kamfanonin Google, da Nokia da sauransu, domin samar da sabon ikon bunkasa ci gaban ayyukan gona a Afirka.

Manazarta sun yi nuni da cewa, kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na sa kaimi ga ci gaban ayyukan gona a Afirka a fannoni uku.

Na farko shi ne fannin kyautata fa'idar harkokin noma. Alkaluma sun nuna cewa, bayan da aka fitar da manhajan ICow, yawan madarar da masu kiwon shanu a Kenya suke samu ya kara da kashi 50 cikin dari, yayin da yawan kudin shiga da suke samu ya karu da kashi 42 cikin dari.

Na biyu shi ne, kawar da cikas da fannin sufuri, da kasuwa ke haifarwa ga samar da amfanin gona, sakamakon jan baya da ake samu a fannin bunkasa muhimman ababen more rayuwa. Kididdiga ta shaida cewa, a cikin farashin takin zamani da manoma ke amfani da su, kudin sufuri ya kan kai kaso 40 cikin dari. More labarai, da yin ciniki ta intanet kuwa ya taimakawa cin moriyar amfanin gona wajen bude hanyar shiga kasuwanni, da kuma rage yawan kudin da a kan kashe ta fuskar sufuri.

Na uku kuwa shi ne, sa kaimi ga aikin tsara manufofin ayyukan gona bisa hakikanin halin da manoma ke ciki. Sabo da yawancin mutanen da manufofin ayyukan gona na Afirka suka fi shafa suna zaune ne a yankunan karkara, ta yadda ba su da damar sanya hannu sosai cikin aikin tsara manufofin. Hakan kuwa ya kan haddasa matsalar tsara manufofi ba bisa hakikanin halin da ake ciki ba. Amma bayan bullar damar amfani da fasahar sadarwa, manoma suna iya samun labarai kai tsaye kan manufofi, da hidimomi, da fasahohi, da farashi ta manhajojin tafi da gidanka. Baya ga samun bukatunsu, masu alaka da fadin gonakinsu, da yawan amfanin gona, da kuma yawan kayayyakin da suka sayarwa. Wanda hakan kan taimaka ga aikin tsara manufofi.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China