An dai kebe ranar 27 ga watan Janairun kowace shekara, a matsayin ranar tunawa da mutane da suka mutu, a sakamakon kisan kiyashin da sojojin Nazi suka aiwatar. A makamanciyar wannan rana a shekarar 1945 ne dai sojojin kawancen kasa da kasa, suka ceto Yahudawan da aka yi garkuwa da su a gidan tsare mutane na Auschwitz Birkenau. A kuma bana MDD ta jinkirta bikin zuwa 28 ga wannan wata, sakamakon hadarin kwararar dusar kankara da aka samu a arewa maso gabashin kasar Amurka cikin wannan mako.
Da yake jawabi don gane da bikin, babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya ce ra'ayin nuna kyama da nuna kiyayya ga Yahudawa ba abu ne da za a amince da shi ba a dukkanin fadin duniya. Kana ya yi kira ga kasashen duniya da su kawar da rashin jituwa daga tushe.
A nasa jawabi shugaban kasar Isra'ila Reuven Rivlin, ya ce cikin manyan dalilin kafa MDD har da daukar matakan tabbatar da magance aukuwar irin wancan kisan kiyashi a nan gaba. (Zainab)