in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira a kara shiga aikin kyautata ababen more rayuwa a Afrika
2015-01-29 10:21:45 cri

Gwamnatin kasar Sin ta nuna fatan ganin kasashe sun rika nuna sahihanci, kamar yadda kasar Sin take yi, domin karfafa gina ababen more rayuwa a Afrika, ta yadda za'a amsa muhimman bukatun Afrika a wannan fanni, in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar, madam Hua Chunying, bayan kungiyar tarayyar Afrika AU da kasar Sin sun rattaba hannu kan wata takardar fahimatar juna MDC game da sufuri, jiragen kasa masu saurin gudu, zirga-zirgar jiragen sama, hanyoyin mota da masana'antu a nahiyar. Bikin sanya hannun ya gudana a ranar Talata a cibiyar AU dake birnin Addis Abeba na kasar Habasha, a yayin zaman taron AU karo na 24.

Takardar MDC na nuna cewa, Sin a shirye take wajen aiwatar da tsarin hadin gwiwa tare da Afrika, kamar yadda shugaba Xi Jinping da faraminista Li Keqiang suka yi fata, ta hanyar taimakon gina hanyoyin layin dogo, hanyoyin mota da kuma kafa hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama na shiyoyi, in ji madam Hua a yayin wani taron manema labarai.

Karfafa sadarwa da dunkulewar Afrika, kawar da duk wani shingen da ke toshe ci gabanta da taimaka wajen samar da wani ci gaba mai dorewa sun kasance daga cikin wasu alkawuranmu, in ji madam Hua. Idan ana son zama mai arziki, dole sai an gina hanyoyi da farko. Wannan wani mihimmin darasi ne na manufar gyare-gyare, bude kofa da ci gaban tattalin arziki cikin saura na kasar Sin a kusan shekaru talatin da suka gabata.

Kasar Sin dai ta gudanar da manyan ayyuka 1046 a Afrika, tare da gina hanyoyin layin dogo na tsawon kilomita 2233 da hanyoyin mota na tsawon kilomita 3530. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China