in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Gambia na neman a hukunta wadanda suka yi yunkurin kifar da gwamnatin kasar
2015-01-08 10:19:35 cri

A jiya ne majalisar dokokin kasar Gambia ta amince da wani kuduri da ke neman hadin kan kasashen duniya na ganin an hukunta wadanda suka yi yunkurin kifar da gwamnatin kasar a matsayin wani mataki na hana abkuwar tashin hankali a kasar nan gaba

'Yan majalisar sun kuma yi kira ga MDD, kasashen Afirka, da kotun hukunta manyan laifffuka ta duniya (ICC) da su tilastawa duk wani dan kasar Gambia da ke huruminsu bin dokokin kasa da kasa da ke neman iznin mafaka, shiryawa ko daukar nauyin duk wasu ayyukan ta'addanci a kasar Gambia.

Har ila, 'yan majalisar sun yabawa sojoji da jami'an tsaro da ke kasar kan yadda suka nuna kishin kasa wajen murkushe harin ta'addanci.

A jawabinsa, shugaban masu rinjiye na majalisar dokokin kasar Fabakry Tombong Jatta ya shaidawa mambobin majalisar cewa, ba abin da zai tsoratar da al'ummar Gambia da jami'an tsaron kasar.

A ranar 30 ga watan Disamba ne wasu da mahukuntan kasar ke dangantawa da 'yan ta'adda kuma 'yan koren kasashen waje da yunkurin kifar da gwamnatin Yahya Jammeh. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China