in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi kira da a kara inganta sha'anin mulki bisa doka a yankin Macao
2014-12-20 16:24:37 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi kira da a kara daukar matakan inganta sha'anin mulki bisa doka a yankin musamman na Macao.

Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan a Asabar din nan a yayin bikin cikar yankin shekaru 15 da komowa karkashin gudanarwar babban yankin kasar Sin, da rantsar da sabon jami'in farko na gudanarwar yankin, ya kara da cewa, yanayin da ake ciki, yanayi ne da al'umma ke burin ganin karin ci gaba, don haka ya zama wajibi a kara azama, wajen karfafa harkokin mulki bisa ka'idojin da doka ta tanada, matakin da zai zama wani ginshiki na bunkasa harkokin mulkin yankin na Macao.

Shugaban kasar ta Sin ya kuma bayyana matukar farin cikinsa, game da abin da ya kira cikakkiyar nasarar da aka samu wajen aiwatar da manufar kasa daya tsarin mulki biyu a yankin na Macao, baya ga nasarar da tsarin gudanarwar yankin ya samu, karkashin manufar cin gashin kai da ke samun karin amincewar al'umma.

A nasa jawabi, sabon babban jami'in gudanarwar yankin Chui Sai On, cewa ya yi, gwamnatinsa za ta ci gaba da kara kaimi wajen tabbatar da mulkin yankin bisa adalci, tare da kwazo a fannin samar da dokoki managarta, da kuma yaki da cin hanci da rashawa. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China