141212-abincin-halal-na-kasar-Sin-2-lubabatu.m4a
|
Kasancewarta daya daga cikin jihohi biyar masu cin gashin kansu na kasar Sin, Ningxia jiha ce mai zaman kanta ta kabilar Hui. 'Yan kabilar Hui a jihar Ningxia sun dauki fiye da kashi 1/3 na yawan al'ummar jihar Ningxia baki daya, haka kuma kashi 1/5 na al'ummar kabilar Hui ta kasar Sin. Don haka ake kira jihar Ningxia jihar musulmi a kasar Sin. A ci gaba da bin mu a ziyarar da Fatimah Jibril ta kai a wasu sassan musulmi na kasar Sin, musamman a jihar Ningxia, don samun karin haske a kan abincin halal na musulmin wurin da kuma al'adunsu.