in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsarin inganta birane na kasar Sin zai haifar da fa'idoji masu yawa,in ji wakilin kasar
2014-11-01 16:39:30 cri
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya ce tsarin inganta birane na kasar Sin, muhimmin mataki ne da zai haifar da karin fa'idoji ga duniya.

Liu Jieyi, wanda ya bayyana hakan ga taron MDD na farko kan ranar birane ta duniya a jiya juma'a, ya ce tuni shirin bukasa birane na kasar Sin ya kai kaso 53.7 bisa dari, kason da ya yi kusa da matsakaicin matakin da ake da shi a duniya baki daya.

Wakilin na Sin ya bayyana manufar kasarsa a fannin gina birane, ciki hadda batun dacewar manufar da bukatun al'umma, tare da kasance bisa tsari mai inganci mai kuma dorewa. A cewar sa hakan ya sanya wannan manufa zama kofar samar da kafar zuba jari ga daukacin kasashen duniya, matakin da kuma zai bunkasa tattalin arzikin duniyar baki daya.

An dai kirkiri wannan rana ta birane ne yayin babban taron nune-nune na duniya da ya gudana a birnin Shanghai a shekarar 2010, da nufin yayata bukatar samar da managartan birane da kyautata rayuwar al'umma. Ta kuma kasance rana irin ta ta farko da MDD ta kebe, bisa kudurin da kasar Sin ta gabatar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China