in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Na'urar bincikin duniyar wata mallakar kasar Sin ta iso gida
2014-11-01 16:34:08 cri
A karon farko cikin kusan shekaru 40, na'urar binciken duniyar wata mallakar kasar Sin ta kammala gwaje-gwaje, ta kuma dawo gida cikin kyakkyawan yanayi.

Hakan dai ya sanya kasar ta Sin kasancewa ta uku bayan kasashen Amurka da Rasha, a jerin kasashen da suka taba samun nasarar gudanar da binciken duniyar wata ta hanyar amfani da na'urar bincike ta zamani.

Na'urar wadda aka yi wa lakabi da Xiaofei, ta sauko ne a wani wuri dake yankin Mongoliya ta gida da sanyin safiyar Asabar din nan.

Kwararru a sashen binciken sararin samaniyar kasar ta Sin sun bayyana cewa aikin wannan na'ura ya hada da gwaji kan fasahohin da za a yi amfani da su yayin ayyukan da na'urar Chang'e-5 za ta gudanar, idan an harba ta a shekarar 2017.

An dai harba wannan na'ura ta Xiaofei ne a ranar Juma'ar karshen makon jiya, ta kuma shafe nisan kilomita 840,000 a sassan doron wata, tare da dakko hotunan duniyar wata, da kuma sararin duniyar bil'adama.

A cewar mataimakin darakta a hukumar lura da karkokin kimiyya da Fasaha, masana'antu da tsaron kasar Sin Mr. Wu Yanhua, gwaje-gwajen da wannan na'ura ta yi sun samar da bayanai masu gamsarwa game da ayyukan da za a sanya gaba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China