in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron WIEF karo na 10 a Dubai
2014-10-29 15:19:21 cri

A jiya Talata 28 ga watan nan ne aka bude babban taron tattalin arzikin al'ummar musulmi ko (WIEF) karo na 10 a birnin Dubai, na hadaddiyar daular Larabawa, wanda ya samu halartar sarkin Dubai Mohammad Bin Rashid Al Maktoum, da firaministan kasar Malaysia Najib Tun Abdul Razak, da shugaban kasar Kazakhstan, da kuma sauran manyan jami'an siyasa na wasu kasashe.

An bude babban taron tattalin arzikin al'ummar musulmi wato WIEF na wannan karo ne a birnin Dubai, za kuma a kwashe kwanaki uku wato daga ranar 28 zuwa 30 ga wata ana gudanar da shi.

Bisa labarin da muka samu, an ce asusun WIEF mai hedkwatarsa a Malaysia, da kuma kungiyar kasuwanci da masana'antu ta Dubai ne suka dauki nauyin shirya taron. Kuma babban takensa shi ne "kafa sabuwar dangantakar abokantaka da nufin samun bunkasuwar tattalin arziki".

A yayin wannan babban taro, wakilai fiye da 2500 daga kasashe sama da 140 za su tattauna kan yadda za a hada kai, da kuma inganta wadatuwar tattalin arzikin al'ummar musulmi a tsakanin kasashensu, kana za su mori alfanun fasahohin da suka samu wajen bunkasa ci-gaban tattalin arzikinsu.

A yayin bikin bude babban taron, shugaban asusun WIEF Musa Hitam ya bayyana cewa, a shekaru 10 da suka gabata, asusunsa ya samu saurin bunkasuwa, inda ya kai wakilai sama da 2800 suka halarci babban taron karon 9 da aka shirya a birnin London, wanda ba a taba ganin irinsa ba a tarihi. Bugu da kari wasu kasashen da ba na musulmi ba ma sun sa himma wajen halartar babban taron, da nufin kara samun dama mai kyau ta gudanar da hadin kan tattalin arziki tare da kasashen musulmi.

Musa Hitam ya ce,

"Wakilai 400 ne kacal suka halarci babban taron na WIEF karo na farko da aka shirya a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia. Bayan shekaru 10 da suka gabata, yawan wakilan da suka halarci babban taron na birnin London ya kai 2800. Na yi imanin cewa, wannan adadi zai haura a yayin babban taron na wannan karo."

Babban jami'in zartaswa na jam'iyyar kasuwanci da masana'antu na Dubai Hamad Buamim ya bayyana cewa, wannan ne karo na farko da aka shirya babban taron na WIEF a yankin Gabas ta Tsakiya, yana sa ido da ganin za a cimma ra'ayi daya kan yadda za a kara azama kan bunkasuwar tattalin arzikin al'ummar musulmi a gun taron.

A nasa bangaren, yayin bikin bude taron, ministan harkokin gida na hadaddiyar daular Larabawa Mohammed al-Gergawi ya ce, yana fatan babban taron na wannan karo zai samar da taimako ga kasashe daban daban, wajen gudanar da hadin kai da neman bunkasuwa.

Al-Gergawi ya ce,

"Ina fatan wannan babban taro zai kasance dandamalin karfafa hadin kai tsakanin kasashe daban daban, a waje guda kuma na yi imanin cewa, za a sanar da manufar musulunci ga duk duniya a yayin babban taron, wato dai batun neman inganta rayuwar jama'a da samar da alheri ga al'umma."

Haka zakila, a yayin da yake nasa jawabi a gun bikin bude babban taron, firaministan kasar Malaysia Najib Tun Abdul Razak, jaddada muhimmancin ilimi ya yi a fannin yunkurin bunkasuwar tattalin arziki. Inda ya nuna cewa, a baya duniyar musulmi ta kirkiro al'adu masu kyau, ta kuma taba shahara sakamakon mayar da hankali kan samar da ilimi. Sai dai, yanzu al'adu sun kasance matsala gaban wasu kasashen musulmi. Najib ya ce,

"Bisa kididdigar da kungiyar kula da harkokin ilmi da fasaha da al'adu ta musulmi ta yi, an ce, yawan maza marasa ilimi a wasu kasashen musulmi ya kai kashi 40 cikin 100, yayin da wannan adadi ya kai kaso 65 bisa 100 a bangaren mata. Har wa yau Asusun al'adu na duniya ya bayar da kididdigar da ta nuna cewa, yawan hasarar tattalin arziki da ake samu sakamakon rashin ilmi da ya shafi karatu da rubutu ya kai dalar Amurka biliyan 1000 a ko wace shekara. Don haka ya kamata mu yi hadin kai matuka tare da kungiyar kula da harkokin ilmi da fasaha da al'adu ta musulmi, da nufin ba da tabbaci ga jama'armu wajen samun ilmi, hakan zai iya taka rawar gani wajen bunkasuwar tattalin arziki da ci-gaban al'umma." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China