in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi babban zabe karo na 11 a Botswana
2014-10-24 16:58:50 cri

A yau Jumma'a 24 ga wata ne, aka yi babban zabe karo na 11 a kasar Botswana dake kudancin nahiyar Afirka tun bayan da kasar ta samu 'yancin kanta. Kafin babban zaben, akwai zaman lafiya a kasar. Manazarta sun bayyana cewa, wannan shi ne babban zabe da aka fi samun 'yan takara a tarihin kasar. Ko da yake watakila jam'iyyar dake rike da mulkin kasar ta lashe babban zaben, amma mai yiwuwa ne yawan kuri'un da za ta samu ba za su yi yawa ba. Yanzu ga cikakken rahoto da Fatima ta bayar.

A wannan babban zaben, ana saran masu kada kuri'a su zabi 'yan majalisar dokokin kasar da na larduna daban daban ta hanyar jefa kuri'a, daga bisani kuma, majalisar dokokin kasar ta zabi shugaban kasar. Baki daya akwai kujeru 57 a majalisar, sannan jam'iyyar da za ta samu sama da rabi kujerun majalisar ita ce za ta kafa gwamnati. Manyan jam'iyyun dake yin takara da jam'iyyar Democratic (BDP) su ne jam'iyyun Congress (BCP) da Umbrella for Democratic Change (UDC). Bisa alkaluman da hukumar zabe mai zaman kanta ta Botswana ta gabatar, an ce, a cikin jama'ar kasar da yawansu ya kai sama da miliyan 2, yawan masu kada kuri'a ya kai sama da dubu 820, kuma an tanadi rumfunan kada kuri'a sama da 2600 a duk fadin kasar. Yayin da yake magana da wakilinmu, babban jami'in watsa labarai na hukumar zaben kasar, Maroba ya bayyana cewa, ana shirye-shiryen babban zaben. Ya ce,

"An riga an tanadi dukkan muhimman kayayyakin zaben, yayin da aka horar da ma'aikatan da za su gudanar da babban zaben. Mun yi imani cewa, za a gudanar da babban zaben lami lafiya. Al'ummar kasar masu son zaman lafiya ne. Ko da yake akwai bambance bambance ra'ayoyin siyasa, amma jama'a za su kada kuri'a bisa tsarin demokuradiyya lami lafiya."

A nahiyar Afirka, an dauki kasar Botswana a matsayin abin koyi a fannin demokuradiyya da rashin cin hanci da rashawa. Kasar ta dade tana zaune cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Jimillar kudin shiga da kowane mutum ke samu a kasar yana sahun gaba a duk kasashen Afirka. Tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai a shekarar 1966, jam'iyyar BDP ce ke mulkin kasar har zuwa yanzu. A cikin babban zaben da ya gabata, jam'iyyar ta samu kujeru 45 daga cikin 57 na majalisar dokokin kasar, wannan ya nuna cewa tana da babban rinjaye a majalisar. Amma ana ganin cewa, a cikin shekaru biyar da suka wuce, yanayin kasar a fannonin siyasa da tattalin arziki ya canja sosai, kuma jama'a suna fatan ganin samun canji a kai a kai, a sabili da haka, jam'iyyar BDP take fuskantar karin kalubale, misali, sabo da gwamnatin Botswana ta dogaro ga albarkatun lu'u-lu'u matuka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar, wannan ya sa gyare-gyaren da gwamnatin ta yi a fannin tattalin arziki ba su sami babban sakamako ba, sannan matasa da yawa ba su da ayyukan yi. Masani kan ilmin siyasa na jami'ar Botswana, mista Sesa ya bayyana wa wakilinmu cewa, ra'ayin masu kada kuri'a na neman samun canji zai yi tasiri a babban zaben. Ya ce,

"Matasa da yawa suna magana kan neman samun sauyi. Wasu mutane suna tunawa da manufofin da gwamnatin kasar ta dauka a da, suna ganin hakan na iya kawo musu koma baya. Wasu kuma suna fatan samun sabuwar gwamnati a kasar. A ganina, idan ma har jam'iyyar BDP za ta sami nasara, to yawan kuri'un da za ta sami ba masu yawa ba ne, kuma za a mai da hankali sosai kan wa zai zama mataimakin shugaban kasar da kuma 'yan majalisar dokoki."

Bugu da kari an kashe kudi da yawa a yakin neman zabe. An labarta cewa, jimillar kudin da jam'iyyun suka kashe domin neman tsayawa takara a babban zaben ta kai dala miliyan 11 baki daya. Jakadan Sin a Botswana Zheng Zhuqiang ya gaya wa wakilinmu cewa, ko wanene ya lashe kujerar shugaban kasar, dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Botswana za ta ci gaba da bunkasa yadda ya kamata. Zheng ya ce, 

"Wannan babban zabe na da ma'ana sosai ga yanayin siyasa na kasar Botswana. Ana tsammani cewa, jam'iyyar BDP dake rike da mulkin kasar ce za ta ci gaba da mulki. Amma ko jam'iyyar BDP ko jam'iyyar adawa ce ta yi nasara, Botswana za ta ci gaba da sada zumunci da Sin. Kuma kasashen biyu na fatan ci gaba da karfafa hadin gwiwa tsakaninsu a nan gaba."

An ba da labarin cewa, masu sa ido kimanin 900 daga kungiyar tarayyar kasashen Afirka (AU), da kungiyar SADC, da sauransu ne za su sa ido kan babban zaben na kasar Botswana. Kuma ana sanya ran cewa, za a gabatar da sakamakon zaben a ranar 26 ga wata. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China