in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin a MDD ya yi kiran a tallafawa kasashe masu tasowa tunkarar kalubale
2014-10-24 14:29:52 cri

Mataimakin zaunanen wakilin kasar Sin a MDD. Wang Min ya yi kira a kan kasashen duniya da su dauki matakai masu kwari domin agazawa kasashe masu tasowa da kuma kasashen da ba su da gabar bakin ruwa, tunkarar kalubalen dake addabar su, ciki har da cutar Ebola mai saurin kashe bil'adama.

Wang Min ya ce, a halin da ake ciki akwai bukatar a taimakawa wadannan kasashe, musamman saboda matsalolin da ake fuskanta kamar tabarbarewar samar da taimakon agaji da kuma, koma bayan ci gaba na tattalin arzikin kasashe, rashin raba daidai na tattalin arzikin duniya, da barazana ta rashin tsaro, da kuma matsalar barkewar cutar Ebola.

Wang ya bukaci kasashen duniya da su taimaka wa kasashe marasa galihu tunkarar matsalolin da ake fuskanta.

Ita dai kasar Sin tana taimakon kasashe masu tasowa, kamar dai yadda yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin kudu da kudu ta tanada, kasar ta Sin ta kuma yi alkawarin za ta kara taimakon da take baiwa kasashe masu tasowa, tare da yin aiki da su kafada da kafada domin taimaka musu tunkarar kalubale na rayuwa. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China