in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A karo na farko an tattauna kan batun gudanar da harkokin mulkin kasa bisa doka a yayin cikakken zama na kwamitin tsakiya na JKS
2014-10-22 17:14:34 cri

An kira cikakken zama na hudu na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwamins ta Sin karo na 18 a nan birnin Beijing kwanan baya, wannan taro mai taken "Gudanar da harkokin mulkin kasa bisa doka" ya jawo hankulan mutane sosai. A cikin shekaru biyu bayan da aka gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar JKS karo na 18, an kori manyan jami'ai fiye da 50 wadanda suke matsayin gwamnoni ko ministocin hukumomin gwamnati daga mukamansu, wannan ya sa al'ummar Sinawa sun nuna gamsuwa sosai kan matakan da sabbin shugabanni suka dauka na yaki da yunkurin neman moriyar son kai da wasu masu hannu da shuni suke yi kamar yadda suke so bisa matsayinsu. Lamarin da ya jawo hankulan kasa da kasa sosai. Wannan ya taka muhimmiyar rawa a matakan da ake dauka na yaki da cin hanci da karbar rashawa yadda ya kamata, to, ta yaya wannan batu wato gudanar da harkokin mulkin kasa bisa doka ya zama muhimmin aiki na sabbin shugabanni?

Yau da watanni biyu da suka gabata, gidan talibijin na kasar Sin, wato CCTV ya sanar da shawarar da kwamitin tsakiya na JKS ya yanke na cewa, an fara binciken tsohon wakilin kwamitin dindindin na hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS Zhou Yongkang bisa doka. A waje daya, an fitar da babban jigon cikakken zama na 4 na kwamitin tsakiya na JKS, wato za a "gudanar da harkokin mulkin kasa bisa doka". Abin da ya alamta cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na kokarin yaki da cin hanci da karbar rashawa da kuma yaki da yunkurin neman moriyar son kai da wasu masu hannu da shuni suke yi kamar yadda suke so bisa matsayinsu. Game da wannan batu, shehu malami Li Chengyan na kwalejin koyon ilmin gudanar da harkokin mulki na jami'ar Peking ya bayyana cewa,

"Ya kamata a sa kaimi ga kokarin kafa sabbin tsare-tsare da tsarin dokoki bayan babban kokarin da aka yi na yaki da cin hanci da karbar rashawa. Wasu matsaloli su kan bullo bayan da aka yi kokarin kawar da cin hanci da karbar rashawa, saboda haka, ya zama wajibi da a kafa wani sabon yanayi, kuma abu mafi muhimmanci na kafa irin wannan sabon yanayi shi ne kokarin gudanar da harkokin mulkin kasa bisa doka."

Bayan da aka samu canjin sabbin shugabanni a kasar Sin yau da shekaru 2 da suka gabata, an kori wasu manyan jami'ai daga mukamansu bayan da aka same su da aikata laifin cin hanci da karbar rashawa. Abin da ya bayyana anniyar sabuwar gwamnati ta daidaita wannan matsala. A ganin wasu kafofin yada labaru, kafa tsarin yaki da cin hanci ya zama wani babban aikin dake jawo hankulan jama'a a wannan cikakken zaman taro. Direktan ofishin nazarin harkokin siyasa na kwalejin koyon ilmin mulkin kasa na kasar Sin Mr. Zhu Lijia ya furta cewa:

"Ta wannan taron da ake yi, ana fatan ba ma kawai za a iya cafke wasu jami'ai wadanda suka aikata laifuffukan cin hanci da karbar rashawa ba, har ma za a iya kafa wani tsarin yaki da laifin cin hanci da karbar rashawa daga asalinsa. Yaki da cin hanci da karbar rashawa shi ne yin rigakafin aukuwar irin wannan laifi, wato kamar yadda aka fadi cewa, za a iya sa ido kan yadda ake tafiyar da ikon mukin kasa bisa doka. Sakamakon haka, za a iya kafa wani yanayi kamar haka, masu hannu da shuni ba su iya, kuma ba su son cin hanci da karbar rashawa ba. A cikin shekara daya da ta gabata, mun koyi darasi sosai daga wannan matsala, muhimmin abu da za mu yi nan gaba shi ne, fitar da dokoki da shari'a dake da nasaba da wannan fanni."

Ban da haka kuma, a gun cikakken zama karo na 3 da aka yi a karshen shekarar bara, sabbin shugabanni sun yanke shawarar zurfafa yin kwaskwarima, matakan da suka dauka sun jawo hankulan al'umma sosai, ciki hadda tabbatar da muhimminci na kasuwanni ta fuskar rarraba albakarun kasa, da sa kaimi ga tsarin gudanar da harkokin mukin kasa bisa doka da zai iya dacewa da zamanin yanzu. Direktan sashin koyar da ilmin shari'a na kwalejin koyon ilmin mulkin kasa na kasar Sin Mr Hu Jianmiao ya ce:

"Muradin da aka gabatar na zurfafa yin kwaskwarima a cikakken zama karo na uku da aka yi a shekarar bara, na da ma'ana sosai wajen kyautata da bunkasa tsari mai halayen musamman na gurguzu na kasar Sin, da sa kaimi wajen neman dacewa da zamanin yanzu a fannin tsari da karfin gudanar da harkokin mulkin kasa. A ganina, sa kaimi ga gudanar da harkokin mulkin kasa bisa doka muhimmin abu ne da suka shafi wadannan ayyuka. Kuma, tunanin Shugaba Xi Jinping na bunkasa dukkan harkokin kasa bai daya, na da muhimmanci sosai kan gudanar da harkokin mulkin kasa bisa doka." (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China