in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sarkin Kano a Najeriya ya kwaskwarima ga masarautar tare da nada sabon Galadiman
2014-10-08 13:41:20 cri

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi kwaskwarima a masarautar tare da nada Aminu Ado Bayero a matsayin Wamban Kano sannan Ahmad Ado Bayero kuma a matsayin Sarkin Dawakin Tsakar Gida.

Haka kuma, An nada Alhaji Abbas Sanusi, wanda kawu ne ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, a matsayin Galadiman Kano, wadda ita ce Sarauta mafi girma na 'ya'yan Sarauta. Alhaji Abbas Sanusi ya maye gurbin marigayi Alhaji Tijjani Hashim ne tsohon Galadiman Kano wanda ya rasu a makon da ya gabata..

Har ila yau Sarki Alhaji Muhammadu Sanusi II ya nada dan gidan marigari Galadiman Kano, Barde Tijjani Hashim a matsayin Dan Isan Kano. Sarkin ya sanar da nadin sarautun ne a fadarsa a karshen makon da ya gabata.

Sarautar Wamban Kano, wadda ita ce ta biyu a daraja a tsakanin 'ya'yan Sarauta, an maye gurbin ta da Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda kafin sabon mukamin sa shike rike da saurautar Sarkin Dawakin Tsakar Gida.

Shi kuma Ahmad Ado Bayero za a maye gurbin Sarautarsa ta da, wato Tafida, da Abdullahi Sanusi, wanda shi ma kawu ne ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Shi dai Barde Tijjani Hashim, an nada shi Dan Isan Kano, ya maye gurbin da Abdullahi Sanusi ya rike a baya.

A gefe daya kuma, duk da barazanar matsalar tsaron da ake fama da shi a jihar, Sarkin Kano ya yi bikin hawan Daushe, tare da shi da sauran 'yan fadarsa.

Murtala daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China