in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummar Xinjiang na taimakawa gwamnati a yakin da take yi da ta'addanci
2014-09-29 14:55:39 cri

Tun lokacin da yankin Xinjiang da ke yammacin kasar Sin ya fara kaddamar da yaki da ta'addanci a lokacin bazarar da ta gabata, al'ummomin kalibu dabam-dabam a yankin suka hada karfi da gwammnati da kuma 'yan sanda da ke yankin a yakin da suke yi da 'yan ta'adda.

Shugaban jam'iyyar kwaminis na yankin Xinjiang Zhang Chunxian ya ce, gwamnatin yankin Xinjiang ta ayyana yaki da 'yan ta'adda na tsawon shekara guda a tsakiyar watan Mayu ne sakamakon karuwar munanan hare-haren ta'addanci da ake samu a yankin na Xinjiang.

Idan ba a manta ba, a tsakiyar watan Yuni wasu mahara guda 3 dauke da adduna suka shiga wani dakin wasanni a birnin Hotan inda suka farma fararen hula da ke wasan dara da kuma karta, ko da yake wasu mutane sun mayar da martani kafin 'yan sanda su iso wurin, inda aka kashe 2 daga cikin maharan, yayin da jami'an tsaro suka kama na ukun.

Yanzu haka 'yan sandan yankin sun sanya lada ga duk wanda ya kawo mata bindiga ko abubuwan fashewa, ko ya sanar da 'yan sanda wasu muhimman bayanai game da 'yan ta'adda a tsawon shekara guda na kamfel din yaki da 'yan ta'adda da yankin ya kaddamar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China