in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rashin cika alkawarin taimakon agaji ya dakusar da ci gaban manufofin MDGs
2014-09-19 14:00:13 cri

Wani rahoton MDD ya yi korafin cewar, rashin cika alkawarin bayar da agaji daga kasashen da suka ci gaba, sun kawo cikas ga ci gaban wasu manufofi takwas wadanda aka shata domin kawar da talauci a karkashin manufofin ci gaba na wannan karnin MDGs.

Rahoton na MDD mai taken "halin da ake ciki a game da huldar raya kasashe ta duniya" ya ce, duk da yake cewa a zahiri an samu nasarar kudurorin da aka shata wadanda suka hada da rage kaifin talauci. Da kuma samar da kafofin ruwan sha kai tsaye ga jama'a, inganta rayuwar wadanda ke zama a unguwar matalauta da kuma tabbatar da cewar, adadin yara mata da maza wadanda ke zuwa makaranta ya yi kunnen doki, to amma rahoton ya yi nuni da cewa, samun nasarori a wasu bangarori a yanzu yana tafiyar hawainiya.

Rahoton ya ci gaba da cewar, duk da yake ana samar da tallafin raya kasa, kawo ya zuwa yanzu ba ta canza zani ba domin kuwa akwai katafaren gibi tsakanin kuduri na 8 da kuma yadda ake aiwatar da ayyukan. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China