in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Musulman kasar Sin sun fara tashi zuwa aikin hajji
2014-09-17 16:36:35 cri

Daga ranar 5 ga watan Satumbar nan ne wasu maniyyata aikin hajji daga nan kasar Sin kimanin su 14,500 suka fara tashi zuwa birnin Makka na kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajji.

Domin tallafawa musulman da za su gudanar da aikin hajjin na bana, gwamnatin kasar Sin ta shirya jigilar alhazan da wasu jiragen sama 94 domin kai maniyyatan birnin Mekka a kuma dawo da su gida bayan sun kammala ibada.

A ranar Larabar nan 17 ga wata ne wasu manyan kusoshi daga bangaren addini, da jami'an gwamnatin kasar Sin, gami da jakadan kasar Saudiyya dake kasar Sin Yahya Al-Zaid suka isa filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Beijing, domin yin ban kwana da wasu daga cikin maniyyatan kasar ta Sin.

Da misalin karfe 7 da rabi safiyar ranar 17 ga watan nan wasu Musulmai su kimanin 300 daga jihar Mongoliya ta Gida, na jiran jirgin da zai kwashe su zuwa birnin Mekka na kasar Saudiyya. Daya bayan daya sun yi musabaha da wasu manyan kusoshin kungiyar Musulmai, da jami'an gwamnati, gami da mista Yahya Al-Zaid, jakadan Saudiya dake kasar Sin, wadanda suka zo domin ban kwana da su.

Bisa la'akari da lafiyar jikin maniyyata da tsaronsu, yawancin maniyyatan kasar Sin na tsakanin shekaru 50 zuwa 75 ne a duniya. Don haka Guo Quanrong dan shekaru 75 ya kasa boye zumudinsa yayin da yake tsokaci kan yadda gwamnatin kasar Sin ta taimaka masa cimma burin da ya sanya duk tsawon rayuwarsa, ya ce,"Wannan ne karo na farko da zan yi aikin hajji, don haka ina murna kwarai da gaske. Zan je Mekka in durkusa don in yi addu'a, zan roke shi ya kiyaye dukkan iyalaina. Jirgin nan na da kyau sosai, ba wata matsala, za a iya kammala aikin hajji yadda ya kamata."

A nata bangaren, wata mata mai suna Ma Lanhua ta bayyana cewa, "Ina zumudi matuka ganin wannan ne karo na farko da zan je Makka, kuma wannan buri ne da na sanya a zuci tun dadewa. Hajji aiki ne mai muhimmaci ga Musulmai don su tsabtata zukatansu. Na gamsu da taimakon da gwamnatin kasarmu ta ba mu, ina ma kasar Sin godiya."

Zuwa yau 17 ga wata, maniyyata 12,000 sun tashi daga kasar Sin zuwa birnin Makka. Ana kuma fatan kammala kwashe dukkanin miniyatan kimanin su 14500 a ranar 20 ga wata.

Don taimakawa masu bin addinin Islama, da basu damar gudanar da aikin hajji yadda ya kamata, hukumar kasar Sin mai kula da harkar addini, da kungiyar Musulmai ta kasar, sun yi hadin gwiwa da wasu sassan gwamnati don daukar matakan da suka shafi fannonin zirga-zirga, da aikin jinya, da samar da masauki.

A cewar Guo Chengzhen, mataimakin shugaban kungiyar Musulman kasar Sin, an tura wasu ma'aikata kimanin 60 a wannan karo wadanda za su rika taimakawa maniyyatan gudanar da aikin hajji, da ba da jinya ga wadanda suka kamu da cututtuka, gami da kokarin tabbatar da tsaronsu. Haka zalika, domin magance kamuwa da cutar fid da jini ta Ebola, an riga an dauki wasu matakai na kandagarki. Mista Guo ya ce,(4)

"Muna da likitoci fiye da 40, wadanda za su iya taimakawa mutanen da suka kamu da cututtuka marasa tsanani. Idan an kamu da wata babbar cuta, za a iya zuwa wani daga asibitocin Saudiyya. A bana mun fi mai da hankali kan magance kamuwa da cutar Ebola, da wani nau'in tarin fuka na musamman da aka fama da shi a Gabas ta Tsakiya."

Rahotanni na cewa ita ma a nata bangare gwamnatin kasar Saudiyya, ta kafa wasu tashoshin binciken lafiyar jiki a cikin filayen saukar jiragen saman ta, don magance shigar cutar Ebola cikin kasar. Dukkan fasinjoji da za su shiga kasar za a yi musu bincike, kana za a kebe duk wanda ake zargi da kamuwa da cutar.

Yayin bikin na ban kwana da maniyyatan, jakadan kasar Saudiyya mista Yahya Al-Zaid ya nuna yabon sa ga gwamnatin kasar Sin, game da taimakon da take baiwa al'ummar Musulmai, ya ce,

"Muna yiwa gwamnatin kasar Sin godiya kan yadda take samar da jirage na musamman a ko wace shekara domin kai maniyyata kasar Saudiyya, shi ya sa na kan zo filin tashi da saukar jiragen sama na yi ban kwana da maniyyatan kasar Sin a ko wace shekara."

Ana sa ran maniyyatan za su gudanar da aikin na hajjin bana daga ranar 3 zuwa 7 ga watan Oktobar dake tafe, sa'an nan su fara dawowa gida kasar Sin daga ranar 10 ga watan dake tafe. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China