in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi wasanni tare da yin mu'amalar al'adu a tsakanin kasa da kasa a gun gasar wasannin Olympics ta matasa a birnin Nanjing
2014-09-11 10:27:46 cri

A matsayin gasar dake yin kira ga matasa daga kasa da kasa da su yi watsanni tare da yin mu'amalar al'adu, gasar wasannin Olympics ta matasa tana da alamar musamman, yanzu ake gudanar da gasar ta shekarar 2014 a birnin Nanjing na kasar Sin, sai a maida hankali ga yadda ake yi mu'amalar al'adu yayin da ake yin wasannin gasar.

Ga wasu 'yan wasa, burinsu na halartar gasar wasannin Olympics ta matasa a wannan karo shi ne kara samun ci gaba da fasahohi a gasanni.

A gun wasan gudu mai tsawo mita 1500 na maza da aka yi a safiyar ranar 24 ga wata, dan wasa daga kasar Kenya mai shekaru 17 da haihuwa Gilbert Kwemoi ya zama zakara da kammala wasa da minti 3 da dakika 41.99, wanda ya zarce na biyu wato dan wasa daga kasar Habasa Mulugeta Asefa da dakika 3. Game da samun wannan sakamako, Gilbert ya ji farin ciki kwarai da gaske, domin wannan ne karo na farko da ya halarci gasar wasanni Olympics ta matasa kuma ya cimma zakara. Ya bayyanawa 'yan jarida cewa,"Ina ji dadi sosai, na warware matsaloli a yayin wasan, na kiyaye matsayin farko tun farko zuwa karshe. Ina begen halartar wasannin Olympics ta kasar Brazil dake tafe a shekarar 2016, kuma burina shi ne karya matsayin bajimta na duniya."

Bayan da 'yar wasa daga kasar Lithuania mai rike da matsayin bajinta na duniya Ruta Meilutyte ta kammala gasar wasan ninkaya mai salon kwado na mita 100 na mata da cimma zakara, ta bayyana cewa, "Babu sauki da samun nasara a gasar wasannin Olympics ta matasa. Ko da yake ba ta yi daidai da wasannin Olympics na balagaru, amma ya kamata 'yan wasa sun yi takara da kansu, da doke kansu. Na nuna gamsuwa ga sakamakon da na samu a wannan karo."

Ga 'yan wasa kamar Gilbert da Meilutyte, gasar wasan Olympics ta matasa ta kasance dandalin shiga wasannin Olympics na duniya, yin takara ya zama burinsu na halartar gasar wasannin Olympics ta matasa ta birnin Nanjing. Amma kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta matasa na birnin Nanjing yana fatan gasar ta zama dandalin yin takara kan wasanni, har ma ta samar da kyakkyawar dama ga 'yan wasa matasa don fahimtar muhimmancin yin hadin gwiwa. Don haka, an kiyaye wasan tawagogin hadin gwiwa a tsakanin nahiya da nahiya a gun gasar wasannin Olympics ta matasa ta birnin Nanjing. Membobin dake cikin tawagogi sun zo daga kasashe daban daban amma nahiya daga, an yi wasa a tsakanin nahiya da nahiya. An yi hakan don sa 'yan wasa daga kasashe daban daban su yi hadin gwiwa, kamar yin wasa, ta haka za su sada zumunta da kasancewa abokai. Dan wasa na takobi daga kasar Sin Yan Yinghui da 'yan wasa biyu daga Koriya ta Kudu da Japan sun zama tawagar biyu ta nahiyar Asiya. A ganin Yan Yinghui, babu muhimmanci ne da samun kyakkyawan sakamako ko a'a, abin mai ma'ana gare su shi ne sada zumunta a tsakanin 'yan wasan uku. Ya ce,"Irin wannan wasa tana cike da yanayin hadin gwiwa a tawaga. A cikin tawagarmu, mun yi hadin gwiwa, mun ji dadin wasan. Idan mu uku gamu da juna a gasa ta nan gaba, babu shakka za mu yi mu'amala da juna. Kana mu yi amfani da tsarin Yogger, mu zama abokai kuma za mu kiyaye tuntuba da juna."

Ban da yin wasanni, an shirya ayyukan bada ilmi da yin mu'amalar al'adu a yayin gasar wasannin Olympics ta matasa dake gudanar a birnin Nanjing na kasar Sin don sada zumunta da fahimtar juna a tsakanin 'yan wasa daga kasashen duniya daban daban. Game da wannan, shugaban tawagar 'yan wasan kasar Kenya kuma mataimakin babban sakataren kwamitin harkokin wasannin Olympics na kasar Kenya James Chacha ya yi tsammani cewa, kamata ya yi a kawar da bambance-bambance a fannin al'adu a gasar wasannin Olympics ta matasa, da kuma sa 'yan wasa matasa su kara fahimta al'adu daban daban. Ya ce,"A gun gasar wasannin Olympics ta matasa, ban da yin wasanni, akwai wani abin mai muhimmanci, wato yin mu'amala a fannonin al'adu da bada ilmi. Muna fatan 'yan wasa matasa za su koyi al'adun kasar Sin, da kai ziyara ga wuraren yawon shakatawa da suka ji ta hanyar rediyo ko ga ta hanyar tufaffi. Wannan ne babban bambanci a tsakanin gasar wasannin Olympics ta matasa da ta balagaru."

A yayin gasar wasannin Olympics ta matasa, an gudanar da ayyukan al'adun kasashe daban daban da dama a kauyen wasannin Olympics na matasa. A matsayin mai daukar bakuncin gasar a wannan karo, kasar Sin ta kafa dakin al'adun kasar Sin a kauyen, inda 'yan wasa daga kasashe daban daban su iya koyi buga kayan kida na gargajiya na Sin, yin rubutu-rubutun gargajiya na kasar Sin ta buroshi da kuma koyi Sinanci. Wata dalibar makarantar sakandare ta birnin Nanjing mai suna Hu Yiling ta yi amfani da hutun lokacin zafi da shiga dakin al'adun kasar Sin don taimakawa 'yan wasa daga kasashen waje wajen koyi yin rubutu-rubutun gargajiya na kasar Sin ta buroshi. Game da aikinta, Hu Yiling ta bayyana cewa,"Yin rubutu-rubutu ta buroshi shi ne al'adun gargajiya na kasar Sin, mutane daga kasashen waje suna son koyi wannan sosai. Ta haka za a kara yin mu'amala a tsakanin Sin da sauran kasashen waja a fanning al'adu, kuma gare ni, wannan ne kyakkyawar dama ta yin kira tare da mutane daga kasashen waje, za a kara karfina na harshen Turanci."

A matsayin 'yar birnin Nanjing, Hu Yiling ta ji dadi sosai domin 'yan wasa daga kasa da kasa sun zo birnin Nanjing, ta ce, "Muna maraba da abokai daga kasa da kasa da su zo birnin Nanjing. A matsayin 'yar birnin Nanjing, na yi alfahari da birninmu ya dauki bakuncin gudanar da gasar wasannin Olympics ta matasa."

Game da ayyukan da ake gudanar a yayin gasar wasannin Olympics ta matasa a wannan karo, mai horaswa na tawagar guje-guje da tsalle-tsalle ta Samoa Valusia Talataina ya nuna yabo ga kwamitin shirya gasar wasannin na Nanjing, ya ce,"Idan aka kwantanta shi da kasarmu, birnin Nanjing tana da wadata. Kasarmu ba ta da albarkatun gudanar da wasannin Olympics. Dukkan abubuwa a nan suna da ban sha'awa, mun gode da kasar Sin, mun gode da birnin Nanjing. An bude idonmu ta gasar wasannin."

'Yan wasa daga kasashe daban daban na duniya suna da buri daban daban na halartar gasar wasannin Olympics ta matasa, kana ra'ayoyinsu ga wasannin sun yi bambanta. Ga shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya Thomas Bach, gasar wasannin Olympics ta matasa ta samar wa 'yan wasa matasa daga kasa da kasa damar yin mu'amala, kana gaya musu cewa, wasanni kyakkyawar hanya ce ta yin rayuwa mai lafiya. Mr Bach ya bayyana cewa,"Ban da yin wasanni, gasar wasannin Olympics ta matasa ta kasance dandalin sada zumunta da fahimtar juna da sanin al'adu iri daban daban na duniya. Kuma za a iya dawo gida tare da abubuwan da aka koya a nan. Ina fatan gasar wasannin Olympics ta matasa za ta taimakawa matasa da su san wasanni yana da muhimmanci ga zamantakewar al'umma, ya kamata su kara yi wasanni da koyi hanyar yin rayuwa mai lafiya."

Gasar wasannin Olympics ta matasa ta samar da dandali na yin takara kan wasanni da sada zumunta da yin mu'amala da juna ga 'yan wasa matasa na duniya. Ta halartar gasar wasannin, za a daga fasahohin 'yan wasa na kasa da kasa, da bude idonsu, kana za a taimake su wajen sada zumunta da koyi yin zaman rayuwa da kansu. A hakika dai, wannan ne ma'anar gudanar da gasar wasannin Olympics ta matasa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China