Yayin da yake ganawa da Masimov, Wang Yang ya bayyana cewa, an samu babban ci gaba ta fuskar fahimtar juna da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Kazakhstan, wadanda suka kawo moriya ga jama'ar kasashen biyu, tare da bada gudummawa wajen samun zaman lafiya da bunkasuwa a yankunansu.
Yayin da yake ganawa da Otorbaev kuwa, Wang Yang ya ce, kamata ya yi kasashen Sin da Kyrgyzstan su kara yin hadin gwiwa don bullo da sabbin fannonin samun bunkasuwar cinikayya a tsakaninsu.
Kana a ganawar da Wang Yang ya yi da Dzidziguri, ya ce, kasar Sin ta zama kasa ta biyar wajen yin ciniki da kasar Georgia, kana kasa ta uku wajen zuba jari ga kasar. Kuma kasar Sin za ta sa kaimi ga kamfanonin kasar da su zuba jari da yin ciniki a kasar Georgia. (Zainab)