in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kenya ya yi alkawarin magance matsalar tsaro domin zaburar da harkokin yawon bude ido
2014-09-01 11:55:15 cri

Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya yi alkawarin tunkarar kalubale na tsaro, musamman a birnin Mombasa dake kasar, domin magance matsalar a wani kokari da kasar ke yi na bunkasa yawon bude ido.

A yayin da yake jawabi a Mombasa, Uhuru ya baiwa masu yawon bude ido da 'yan kasar ta Kenya tabbacin cewar, za'a dauki matakan tsaro domin samar da cikakkar kariya ga wuraren bakin ruwa, inda baki ke kai ziyara.

Kasar ta Kenya dai ta fuskanci matsalar hare-hare da gurnet a 'yan watannin da suka wuce, a wuraren da suka hada da babban birnin kasar Nairobi da kuma arewacin Kenya da garin Mombasa dake bakin ruwa, hare-haren sun hada da kashe wasu mutane fiye da 95 a yankuna gabar bakin ruwa na kasar, a watan Yuni da Yuli.

A sakamakon wadannan hare-hare, harkokin yawon bude ido na kasar sun sami koma baya, musamman tun daga shekarar 2011, bayan da kungiyar tsagera ta al-Shabaab ta sace wasu masu yawon bude ido a tsibiran Lamu da kuma sace wadansu masu taimakon sa kai na kasar Spain.

Kididdiga ta nuna cewar, adadin masu yawon bude idon da ke shigowa kasar daga kasar waje ya ragu da kashi 15.8 bisa dari, idan aka yi la'akari da cewar, a shekarar 2012, baki sun shigo kasar har miliyan 1.78, to amma a shekarar 2013, sai adadin bakin suka yi kasa, zuwa miliyan 1.49, hakan ana ganin ba ya rasa nasaba da karin hare-hare na 'yan ta'adda. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China