in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe gasar wasannin motsa jiki na Olympics na matasa karo na biyu a birnin Nanjing
2014-08-29 16:11:58 cri

A daren jiya Alhamis 28 ga wata aka rufe gasar wasannin motsa jiki na Olympics na matasa karo na biyu a birnin Nanjing na kasar Sin. Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci bikin, shugaban kwamitin Olympics na kasa da kasa Thomas Bach ya sanar da rufe gasar a hukumance.

A wajen bikin rufe wasannin, an yi raye-raye da wake-wake mai taken "Kuruciya". Abin da ya nuna fatan samun bunkasuwar bil Adam nan gaba ta hanyar yaduwar wasannin Olympics na matasa.

"A matsayina na wakilai mambobi 204 na kwamitin Olympics na kasa da kasa, ina son nuna godiya ga birnin Nanjing, har ma kasar Sin. Lokacin ban kwana ya yi, ina sanar da cewa, an rufe wannan gasar Olympics ta matasa ta lokacin zafi ta shekarar 2014."

Nuna godiya ga Nanjing, har ma kasar Sin. A lokacin da Mr. Thomas Bach ya yi shelar rufe wannan gasar, ya kuma nuna godiya ga masaukin gwamnatin kasar da jama'arta a madadin mambobin kwamitin Olympics na kasa da kasa, kuma ya nuna gamsuwa sosai ga gudunmawar da birnin Nanjing ya bayar a wannan karo.

Ban da haka, 'yan wasan motsa jiki sun mikawa ma'aikatan sa kai furanni a gun bikin domin nuna musu godiya ga aikin da suka yi.

Ma'aikata masu aikin sa kai kimanin dubu 120 ne suka ba da hidima ga gasar da sauran fannonin dake da nasaba da gasar. Wadannan ma'aikata sun nuna kokari wajen ba da gudunmawarsu ta hanyar nuna fahasa da alamar musamman na gasar a wannan karo mai suna "Lele". Hakan ya sa, Mr Bach ya bayyana sau da dama cewa, Nanjing wurin na da kyau wajen aiwatar da wannan gasa, 'yan wasan motsa jiki sun dandani abubuwa masu kyau, kuma suna fatan yada wadannan fasahohi ga sauran mutane.

A gun bikin rufe wasannin, 'yar wasan nunkaya ta kasar Sin Shen Duo, a madadin sauran 'yan wasan motsa jiki na kasashen 204 da 'yan wasannin motsa jiki kimanin 3800, ta karanta wani jawabi inda ta yi alkawarin samar da wata duniya mai kyau cikin lumana ta yin amfani da karfin motsa jiki. Haka kuma, a wannan karo an yi mu'ammala da tuntubar juna cikin ayyukan motsa jiki daban-daban da dai sauran ayyukan al'adu, wadanda ba su yi la'akari da asalin kasa da jinsi ba. Abin da ya fi nuna muhimmanci shi ne, tawagar masaukin kasar Sin dake kunshe da 'yan wasan motsa jiki 120 sun shiga wadannan gasanni, inda suka samu sakamako mai kyau cikin wasu gasanni, watakila za a iya kallo fasahohinsu a gasar Olympics a nan gaba.

Bikin nuna fasahohi mai taken "Kuruciya" na jaddada kuzari da karfin matasan. Mawakan matasa da dama na kasar Sin sun rera wakoki masu dadin ji na bayyana al'adun gargajiya na birnin Nanjing da na kasar Sin.

A gun bikin, masaukin gasa na karo mai zuwa birnin Buenos Aires na kasar Argentina ta nuna wani gajeren fim domin gabatarwa dukkan duniya tunaninta na gudanar da gasar nan gaba, a karshe kuma, shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Lionel Messi ya gayyaci dukkan matasan duniya da su kai ziyara a Argentina.

An fi son hangen nesa a lokacin da ake waiwayar tarihi. A yayin da wata yarinya ta taba fuskar wata wayar salula ta zamani, wutar yola ta gasar ta mutu sannan a hankali. Ana kuma jin bacin rai kadan sabo da za a yi ban kwana da juna.

Shugaba kwamitin wasannin Olympics na duniya Thomas Bach wanda ya gayyaci dukkan mutanen kasashen duniya da su yi amfani da wayoyinsu na salula su dauki hotuna da kansu a yayin bikin bude gasar, shi ma ya kirkiro sabon abu a yayin bikin rufewa, wato ya gayyaci wadanda suka hallara bikin da su yi amfani da wayoyin salula su dauki hotunan mutane, ko sun san juna ko ba su san juna ba wadanda suke zaune tare domin ajiye karshen lokacin gasar a cikin zuciyarsu.

A matsayin wani aikin gwaji na kungiyar IOC, gasar Olympics ta matasa karo na biyu da aka yi a Nanjing ta sami karbuwa sosai, Sinawa fiye da miliyan 200 sun kalli bikin budewa. Labaran da suka shafi rana ta farko ta gasar sun yadu zuwa ga mutane fiye da miliyan daruruka. Bisa bincike da kwamitin IOC ya yi an ce, mutane fiye da kashi 30 cikin dari na dukkan duniya sun san kasancewar gasar Olympics ta matasa a duniya.

Wakar mai taken "Baiwa gobe haske" ta gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta matasa ta Nanjing ta yi kama da wannan wasa wadda ke bayyana kyakkyawar fatan ga wasannin motsa jiki da al'ummar bil Adam. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China