in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron tunawa da cika shekaru 110 da haihuwar marigayi malam Deng Xiaoping
2014-08-20 20:52:21 cri
A safiyar yau Laraba 20 ga wata, kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya kira taron tunawa da cika shekaru 110 da haihuwan marigayi malam Deng Xiaoping a babban dakin taron jama'a.

A lokacin jawabin sa wajen taron shugaban kasar Sin Xi Jinping ya waiwayi babban sakamakon da malam Deng ya samu a cikin rayuwarsa, kuma ya bayyana babbar gudummawar da malam Deng ya bayar ga juyin mulki da bunkasuwa da kuma yin kwaskwarima a kasar Sin. Shugaba Xi ya jaddada cewa, abin dake gaban kome da malam Deng ya bayar ma kasar shi ne zaman al'ummar gurguzu mai alamar Sin da jam'iyyar Kwaminis ta Sin da jama'ar suka kafa bisa jagorancinsa, da kuma tunaninsa.

Babbar alamar tunaninsa ita ce, gudanar da ayyuka bisa hakikanin yanayin da ake ciki, da yanayin da duniya ke ciki, da kuma yanayin da kasar Sin take ciki, don haka inji Shugaba Xi, ya kamata a tsaya tsayin daka kan ra'ayin neman gaskiya daga abubuwan hakika, da tafiyar da aiki ta hanyar dogaro kan jama'a da kulawa da su, da kuma neman 'yancin kai ba tare da tsangwama ba.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China