in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin kasar Chadi sun ceci mutane 85 da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su
2014-08-18 15:06:06 cri

Bisa labarin da muka samu a ranar 16 ga wata, an ce, sojojin kasar Chadi sun kubutar da wasu mutane 85 da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su a makon jiya, a yayin da ake fuskantar matsalar cutar Ebola mai sauki kisa a yammacin Afirka, bai kamata a yi watsi da kalubalen ta'addanci da 'yan ta'adda ke haifa wa a wannan yanki ba.

A karshen makon jiya ne, kungiyar dakaru masu ra'ayin kaifin kishin Islama a kasar Nijeriya wato Boko Haram suka kai wani mummunan farmaki a arewa maso gabashin kasar, inda suka kama matasa kusan dari tare da yin garkuwa da su, galibin su maza, da wasu mata kalilan. Wadanda suka ganewa idonsu lamarin sun bayyana cewa, an tafi wadannan matasan zuwa kasar Chadi, wasu mazaunan wurin sun bayyana cewa, mutane 28 sun rasa rayukansu yayin da dakarun suka kai musu farmaki, baya ga gidaje da dama da suka kona. Bayan aukuwar lamarin, sojojin kasar Nijeriya sun gudanar da bincike, amma ba su gano wadanda aka yi garkuwa da su ba. Ya zuwa ranar 16 ga wata bisa agogon wurin, sojojin kasar Chadi sun kama wata motar daukar kayayyaki da suke shakkau a kanta a wata tashar binciken ababan hawa, yayin da sojojin suka binciki motar yadda ya kamata, sun gano mutane da yawa a ciki da aka yi garkuwa da su, inda nan take kuma dakaru 6 da suka yi garkuwa mutanen suka gudu a kan babur. Bayan haka kuma, an tabbatar da cewa, a aikin da sojojin kasar Chadi suka gudanar a wannan karo, an ceci maza 63 da mata 22 cikin wadanda aka yi garkuwa da su a makon jiya a kasar Nijeriya. A halin yanzu dai, wadannan matasa 85 suna hannun hukumar tsaron kasar Chadi, kuma har yanzu ba a tabbatar da lokacin da za su dawo gida Nijeriya ba tukuna. Duk da cewa, akwai wasu mutane fiye da 30 da ke hannun dakarun na kungiyar Boko Haram a halin yanzu, wadanda ba a san inda suke ba.

Ya kamata a ce, wannan ya zama wata babbar nasara da kasar Nijeriya da kasashe makwabtaka suka samu a hadin gwiwar da suke na yaki da ta'addanci, amma a halin yanzu suna fuskantar kalubale mai tsanani, domin ba a san makomarsu ba a nan gaba. Musamman ma a yankin da ke arewa maso gabashin Nijeriya da ya kasance cibiyar kungiyar Boko Haram, wadda dakarunta suka kware wajen aiwatar da shirye-shiryensu, ban da wannan kuma, ana aiwatar da wannan yanki a dab da yankin tabkin Chadi da ke kan iyakar Nijeriya da Chadi, da kuma iyakar Nijeriya da Kamaru, wannan ya sa 'yan ta'addan ke boya cikin sauki tare da kai hare-hare a duk lokacin da suke so a wannan yanki, sakamakon haka ne ma, sojojin gwamnatocin wadannan kasashe suke fuskantar wahala wajen gurgunta ayyukan 'yan ta'addan. Ko da yake a da kasashen Nijeriya da Chadi da Kamaru sun taba kafa wata rundunar hadin gwiwa, tare da daddale wasu yarjejeniyoyi domin hada kai wajen yaki da ta'addanci, inda suka tabbatar da yin musayar bayanai tare da daukar matakan soja tare, amma har yanzu ba su samu nasara ba. Musamman a 'yan shekarun baya, dakarun kungiyar Boko Haram suna kara ratsa dazuzzuka da tabkuna, tare da tsallaka kan iyakar kasa suna kai farmaki, a wani lokaci ma dakarun su kan buya a wannan yanki, inda su kan yi jigilar kayayyaki da makamai, matsalolin da har yanzu ba a iya warware su yadda ya kamata ba.

A cikin watanni uku da suka gabata, 'yan kungiyar sun sha kai hare-haren kunar bakin wake a Abuja, babban birnin kasar Nijeriya, da birnin Kano wani muhimmin birnin da ke arewacin kasar, da yankin arewa maso gabashin kasar, tare da tada rikicin ta'addacni ba zato ba tsammani, ban da wannan kuma, kungiyar Boko Haram ta kara kai hare-hare a iyakokin Kamaru da Chadi da dai sauransu, wannan ya zama wani sabon kalubale ne yayin da ake fama da ayyukan ta'addanci. Ban da wannan kuma, kungiyoyin 'yan ta'adda sun bullo da wani salo na kama tarin jama'a domin yin garkuwa da su, sabo da ta hakan ne suke iya jawo hankulan kasashen duniya cikin ruwan sanyi, kamar lamarin yin garkuwa da dalibai 'yan makarantan mata na Chibok da lamarin wannan karo da aka kama matasa kusan dari domin yin garkuwa da su.

Sabo da haka ne ana iya cewa, ba a magance kalubalen ta'addanci da ake fuskanta a Nijeriya ba, haka kuma ba a daina kai farmaki ba duk da matsalar cutar Ebola da ake fuskanta. Ko da yake an samu lafawar kalubalen ta'addanci cikin gajeren lokaci, amma idan aka yi hagen nesa, ana iya ganin cewa, yayin da babban zabe da zaben jihohi ke kara kusanto wa a Nijeriya, batun ta'addanci zai zama babban kalubale na farko a wannan yankin da Nijeriya take ciki. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China