A kalla mutane 33 ne suka mutu a wata turoroniya sakamakon wani kallon kade-kade a bakin ruwa da aka gudanar a Conakry, babban birnin kasar Guinea, kamar yadda kafar yada labaran kasar suka sanar.
Hadarin da ya auku ne a ranar Talata, lokacin da jama'a wadanda suka yi dafifi wajen kallon raye-rayen da aka shirya, musamman domin bikin sallah karama, suke ficewa filin kallon ta wata dan karamar hanya mara fadi, kuma wadansu daga cikin su suka fadi a kasa wanda a nan aka tattaka su, in ji majiyar.
Dubban jama'a ne musamman matasa da yara kanana suka je kallon kade-kaden na wadansu fitattun makadan zamani 'yan kasar.
Gwamnatin kasar Guinea dai ta kira wannan al'amari a matsayin wani tashin hankali, kuma take ta salami jami'an da ke kula da cibiyar shirya wannan wasa, kuma shugaban kasar Alpha Conde ya sanar da mako daya a matsayin zaman makoki ga wadanda suka mutu. (Fatimah)