in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai bambancin ra'ayi kan muhimman batutuwan da za a tattauna tsakanin Amurka da kasashen Afirka
2014-07-30 16:54:46 cri

Fadar White House ta kasar Amurka ta sanar da cewa, za a shirya taron koli na kasar Amurka da kasashen Afirka karo na farko, a ranekun 5 da 6 ga watan Agusta a birnin Washington, taron da ake fatan zai karfafa mu'ammala tsakanin Amurkan da kasashen Afirka a fannonin siyasa da tattalin arziki.

Da dama daga manazarta dai na cewa, a baya an taba gabatar da wani taron koli tsakanin kasar Amurka da kasashen Afirka, lokacin da majalisar dokokin Amurka ta zartas da dokar AGOA, game da bunkasuwar Afirka, da damar da take da ita a shekarar 2000.

Kana bayan shafe shekaru 14 da hakan, Amurka ta sake gabatar da wannan batu, bisa dalilinta na hangen bunkasar kasashen nahiyar. Sai bambancin ra'ayoyi dake tsakanin sassan biyu, wajen tinkarar muhimman batutuwa da za a tattauna a yayin taron kolin, ya sanya ana nuna damuwa, da shakku kan ko Amurka za ta iya nuna halin ya kama ta wajen sauraren muryar nahiyar Afirka ko kuwa a'a?

Tun dai bayan shiga sabon karnin da muke ciki, saurin bunkasuwar tattalin arzikin nahiyar Afirka, da makomar kasuwanninta a nan gaba, sun jawo hankulan kasashen duniya. Inda a shekarar 2006, aka cimma nasarar shirya taron koli a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, wanda ya kafa wani sabon tsari na yin mu'ammala tsakanin kasashen duniya da Afirka. Daga bisani kuma aka sake shirya jerin tarurrukan koli tsakanin Afirka da wasu kasashe da kungiyoyi, ciki har da Koriya ta kudu, da EU, da kasar India, da kasashen Kudancin Amurka, da Japan da dai sauransu.

Wannan mataki dai ya sanya wasu manyan kasashe dake da tasiri a duniya, ko a yankunan da suke soma sha'awar bunkasa dangantakar dake tsakaninsu da nahiyar Afirka ta hanyar shirya taron koli. Mai yiwuwa ne kuma sakamakon hakan ne ya sanya kasar Amurka, wadda ta dade ta kasa kulawa da dangantaka a tsakaninta da kasashen Afirka har na tsaron shekaru goma da wani abu na fatan za ta iya kyautata dangantakar dake tsakaninta da nahiyar Afirka ta hanyar shirya taron koli a tsakanin sassan biyu.

Sai dai fa a hannu guda manazarta na ganin cewa, akwai sabani da yawa game da shirya wannan taro na koli tsakanin kasar Amurka da nahiyar Afirka.

Wato da farko dai sassan biyu suna da bambancin ra'ayi kan muhimman batutuwan da za a tattauna kan su a yayin taron koli. Hasali ma dai fadar White House ta bayar da wata sanarwa a farkon shekarar da muke ciki, inda ta ce za a mayar da hankali kan karfafa cinikayya, da zuba jari da Amurka za ta yi a nahiyar Afirka a yayin taron. Game da haka, manazartan kasashen Afirka sun nuna cewa, Amurka na dora muhimmanci kan batutuwan da suka shafi makamashi, da tsaro da kuma cinikayya, da nufin kiyaye moriyarta a kasashen ketare, da kuma neman kasuwanni a kasashen na ketare, da nufin farfado da masana'antunta na kere-kere.

A tsakiyar watan Yunin wannan shekara ma, a yayin da take tattaunawa da wasu kungiyoyin kasashen Afirka masu zaman kansu, kan muhimman batutuwan taron na koli, kamar yadda ta kan yi a da, kasar Amurka ta sake nanata kudurin tana dora kulawa, kan batutuwan da suka jibanci gudanar da manufofin da suka dace, da yaki da cin hanci da rashawa, da kara bayyana ayyukan gwamnati karara.

Ko da yake wadannan batutuwa na janyo hankulan kasashen Afirka da dama, a hannu guda ba su da dacewa da bukatun nahiyar. Abubuwan da suka fi muhimmanci ga yawancin kasashen Afirka su ne, zakulo hanyoyin inganta yanayin da suke ciki na neman bunkasuwar tattalin arziki, da na samun bunkasuwa daga dukkanin fannoni, da kuma rage yawan matalauta, da kuma kyautata zaman rayuwar jama'a.

Na biyu, kasashen Afirka suna da shakkar kan sahihancin manufar Amurka, kasancewar ba za a gudanar da shawarwari tsakanin shugabannin Amurka da kasashen Afirka ba a yayin taron koli, bisa dalilin cewa hakan ba shi da wani amfani. Kana kasashen Afirka na da shakku kan matsayin Amurka game da kasashen Afirka, da kuma burinta na shirya taron, kamar batun ko da gaske Amurkan na fatan sauraren hakikanin bukatun daukacin kasashen Afirka, da kuma ra'ayoyinsu.

Ban da wannan kuma, Amurka ta hana wasu kasashen Afirka halartar wannan taron koli, ciki har da wasu kasashe dake da dangantaka mai rauni da Amurkan, da wadanda aka dakatar da matsayin su na mambobin kungiyar AU.

A ganin manazartan kasashen Afirka, wannan matakin da Amurka ta dauka, zai iya haifar da illa ga kasashen Afirka, musamman wadanda ke neman hadin kai da burin farfadowa. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China