in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ingila ta mika akwatunan nadar bayanan jirgin saman MH17 ga kasar Netherlands
2014-07-31 16:50:08 cri
Kakakin fadar firaministan kasar Ingila ya bayyana cewa, Ingila ta mika akwatunan nadar bayanan jirgin saman nan na kasar Malaysia mai lamba MH17, ga masu bincike na kasar Netherlands. Ana kuma sa ran gabatar da sakamakon binciken nasu nan da mako mai zuwa.

An ce tun da fari kwamitin tsaron kasar Netherlands ya mika akwatunan nadar bayanan guda biyu, ga cibiyar binciken hadarin jiragen sama ta kasar Ingila ne, da fatan masana a fannin hadarin jiragen sama na cibiyar za su gudanar da bincike, da nazarin da ya dace.

Ban da wannan, kakakin fadar firaministan kasar Ingila ya bayyana cewa, kasarsa ta ja hankalin dakarun sa kai dake gabashin Ukraine, da su datakar da tada zaune tsaye, tare kuma da fatan gwamnatin kasar Ukraine, za ta kokarta wajen samar da tsaro ga tawagar masu bincike ta Netherlands da Australia. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China