Mr Xi ya bada wannan umurni ne a yau Alhamis 24 ga wata, lokacin taron talibijin da wayar tarho na tunawa da cika shekaru 60 da kafa kungiyar a nan birnin Beijing.
Shugaba Xi ya jaddada cewa, kungiyar samar da sayar da kaya na da muhimmanci sosai wajen bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kauyuka wanda a bana ta cika shekaru 60 da kafuwa.
A cewar shi, cikin shekaru 60 da suka gabata, kungiyar ta taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga bunkasa aikin noma da kauyuka, da tabbatar da samar da kayayyaki, da ba da hidimoni ga mutanen dake kauyuka da birane da sauransu.
Shi ma a nasa bangaren Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya tunatar da cewa, kungiyar tana da dogon tarihi a yanzu haka kuma, tana da fifiko na musamman na tallafawa manoma. Don haka ana fatan kungiyar za ta kara ba da gudummawa wajen bunkasa aikon noma na zamani, da taimakawa rayuwar manoma da dai sauransu.(Fatima)