in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Arewacin Najeriya na kokarin kiyaye al'adun tarihi
2014-07-24 19:19:46 cri


A halin yanzu ana gudanar da kasaitaccen bikin baje-kolin kayan tarihi na kasashen Afirka na shekara ta 2014 a dandalin Eagle Square dake Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. Wakilinmu Murtala ya ruwaito mana wani bayani, dangane da yadda jihohin arewacin Najeriya suke kokarin kiyaye al'adunsu na gargajiya.

Arewacin Najeriya, wani muhimmin yanki ne dake kunshe da kyawawan al'adun tarihi da dama, hakan ya sa kokarin da ake na kare al'adun gargajiya da kayan tarihin yankin daga bace wa ya zama wani babban batu ga al'ummar yankin.

A zantawar da na yi da masu fasaha gami da 'yan kasuwa wadanda suka zo daga arewacin Najeriya don halartar bikin baje-kolin kayan hannu na wannan shekara, na fahinci cewa, jihohi da yawa na mayar da hankali sosai kan kare al'adun tarihi.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China