in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafafen yada labarai a Venezuela na mai da hanakali ga batun kasancewar Maradona sabon kocin kasar
2014-07-11 16:25:08 cri

Kafafen yada labarai a kasar Venezuela sun fidda bayanai daban daban kan batun da ake yi, na yiwuwar shahararren tsohon dan kwallon kafar kasar Argentina Diego Maradona, ya kasance sabon kocin kungiyar kwallon kafar kasar.

A ranar Talata makon jiya ne dai Maradona ya bayyana cewa, zai tattauna batun aiki a matsayin mai horas da 'yan wasan kasar ta Venezuela, shi da shugaba Nicolas Maduro a ranar 13 ga watan nan na Yuli, wato bayan kammalar gasar cin kofin duniya a Brazil.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa tuni Maradona, ya bayyana yiwuwar karbar wannan aikin, tun bayan da kocin kasar Cesar Farias ya yi murabus daga mukamin sa cikin watan Nuwambar bara.

A yayain wata tattaunawa da ya yi da wata kafar yanar gizo mai suna Lavinotinto.com, Maradona ya ce yana fatan yin aiki da 'yan kwallo masu hazaka, wadanda zasu daga martabar Venezuela. Maradona ya kara da cewa, gasar cin kofin duniya ta yi rashi na halartar kasar Venezuela.

Sai dai a wani labarin mai alaka da wannan, wata kafar yanar gizo ta rawaito hukumar kwallon kafar kasar ta Venezuela ta wata sanarwa, na cewa bata yi wani shiri na daukar Maradona a matsayin kocin kungiyar kasar ba. Sanarwar ya kara da cewa wannan batu ne da za a tattauna bayan kammala gasar cin kofin duniya dake daf da kammala yanzu haka.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China