in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai bukatar kyautata hanyoyi a nahiyar Afrika
2014-04-24 17:15:51 cri

Wani karin magana na kasar Sin na cewa, idan ana fatan samun arziki, ya wajaba a kafa hanya. A nahiyar Afrika, kasashe da dama na fatan kyautata hanyoyinsu domin sa kaimi ga bunkasuwar al'ummun su. A halin yanzu dai kamfanonin Sin da dama sun ci gaba da taimakawa aikin gina hanyoyi a Afrika. Ya zuwa yanzu, hanyoyin mota da na jiragen kasa da dama na kasashen Afrika na cikin wani mawuyacin hali, matsalar dake bukatar jari mai tarin yawa idan har ana fatan gyara su. Yawancin irin wadannan hanyoyi an gina su ne tun lokacin Turawan mulkin mallaka, wadanda suka hada wuraren da ake hakar ma'adanai da tasoshin jiragen ruwa.

Bisa wata kididdigar da bankin raya Afrika ya fitar, an ce yawan hanyoyi dake nahiyar Afrika bai wuce kashi 1 bisa 5 na wadanda ke daukacin kasashe masu wadata ba, wanda hakan ya sa yawan kudin da ake kashewa wajen sufuri ya ninka kashi 63 bisa dari, in an kwatanta da na kasashe masu wadata. Ba shakka hakan ya kawo cikas matuka ga karfin takarar kasashen na Afrika.

Ban da wannan, kididdigar ta nuna cewa yawan kudin da kasashen Afrika suke kashewa wajen sufuri, ya kai kashi 30 zuwa 50 bisa dari na dukkan kayayyakin da suke fitarwa zuwa kasashen ketare, har ma a wasu kasashe 16, wannan adadi ya kai kashi 3 bisa 4, ciki hadda Zimbabwe, da Sudan ta kudu, da Mali, da Niger da dai sauransu.

Hakika wannan matsala ta kawo cikas ga harkokin cinikayya tsakanin kasashen Afrika, inda yawan kudin da ake samu a wannan fanni ya kai kaso 11 cikin dari. A ganin wasu masana, wannan adadi zai karu, idan an kyautata hanyoyi. An kuma yi kididdigar cewa, hidima da ake gudanarwa kan sufurin fasinjoji bata wuce kaso 2 cikin dari ba, in an kididdige dukkan sha'anin sufurin jiragen kasa a nahiyar ta Afrika, kuma wannan adadi ya ragu a cikin shekaru da dama da suka wuce. Dalili kuwa shi ne kudin da za a kashe wajen kula da na'urorin hanyoyin jiragen kasa ya yi sama sosai, ta yadda in har babu tallafi daga gwamnati, farashin tikitin wannan hanya ta sufuri zai karu warai, ta yadda fasinjoji ba za su iya biya ba.

A hannu guda kuma akwai rahotanni da ke nuna cewa, yanzu tattalin arzikin Afrika na samun ci gaba, da kashi 5 bisa dari a kowace shekara, amma duk da haka wasu shugabannin Afrika na nuna damuwa sosai kan karancin isassun hanyoyi, matsalar da ta iya hana ci gaban tattalin arzikin bada gudummawa ga ci gaban al'umma.

Bankin raya Afrika, da shirin kawancen raya Afrika, da kungiyar tarrayar Afrika ta AU, a wani kokari nasu na gudanar da aikin raya manyan ababen more rayuwa, cikin watan Yulin shekarar 2010, sun yi yunkurin habaka ginin manyan hanyoyin mota da na jiragen kasa, ta yadda za a sauya mawuyacin halin da ake ciki a yanzu.

A wannan aiki, batun aikin hanyar mota da za ta hada birnin Algiers hedkwatar kasar Algeria, da birnin Legas, birnin mafi girma a tarayar mai tsawon kilimita 4500, ya fi kowanne janyo hankalin al'umma. Wannan hanya da aka yiwa lakabin hanyar da ta ratsa Sahara, yanzu haka an kammala kaso 85 bisa dari na ginin ta, ana kuma sa ran gama ta cikin wannan shekara da muke ciki.

Ba shakka wannan hanya za ta kawo amfani wajen sa kaimi ga ciniki tsakanin arewacin Afrika, da yankunan dake kudu da Sahara baki daya. Ban da haka kuma, an kafa wasu hanyoyi a wurare daban-daban a nahiyar ta Afirka. Alal misali, a kasar Kenya, kasa mafi girma ta fuskar tattalin arziki a gabashin Afrika, ana gudanar da aikin kafa manyan ababen more rayuwa, dake lashe kudi kimanin dalar Amurka biliyan 25, ciki hadda wata hanyar da za ta hada kasashen Kenya, da Sudan ta kudu da Habasha.

Haka zalika, bankin raya Afrika na tattara kudi na musamman domin gina hanyoyi a tsakiyar nahiyar. Ban da haka, bankin ya sanar da gabatar da takardun basussuka har na dala biliyan 22 a Afrika, domin ba da taimako wajen gina manyan ababen more rayuwa, za kuma a kebe wasu kudi na daban, domin kafa hanyoyin mota da jiragen kasa, wadanda yawancinsu za a yi amfani da su a gabashi da tsakiyar Afrika.

Gina ingantattun hanyoyi, ba ma kawai zai taimaka wajen kyautata halin da jama'ar Afrika ke ciki ba ne ta fuskar sufurin kayayyaki, da yin shawarwari, da bunkasa sha'anin yawon shakatawa kadai, a'a hakan zai ma taimaka wajen sa kaimi, ga habaka harkokin cinikayya, tare da haifar da amfani da zaman rayuwar jama'a a yau da kullum. Kuma kasar Sin na taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar wannan aiki.

Jaridar Der Spiegel ta kasar Jamus ta ba da labarin cewa, kamfanonin kasar Sin na da muhimmanci sosai, ga aikin kafa manyan na'urorin hanyoyin jiragen kasa a Afrika. Yanzu haka a kasar Kongo Kinshasa, kamfanoni biyu na kasar Sin sun daddale yarjejeniyar da za ta lashe kudi har dalar Amurka biliyan 9, da wani kamfanin hakar ma'adanin tagulla, domin kafa hanyoyin jiragen kasa da na mota.

Dadin dadawa, kasar Kenya ta sa hannu kan wata yarjejeniya da kasar Sin, ta dala biliyan 5, domin shimfida wata hanyar Malaba dake da tsawon kilomita 952, wadda za ta hada Mombasa tashar jiragen ruwa mafi girma a Kenya da garin Malaba dake makwabtaka da kasar Uganda.

Ko da yake, wasu kafofin yada labaru da 'yan siyasa na kasashen yamma, ko na nahiyar ta Afrika na zargin cewa, Sin na baiwa kasashen Afrika taimako ne da zummar kwashe albarkatunta, a hannu guda masu wannan zargi, ba za su iya musanta muhimmiyar gudunmawar da Sin take baiwa nahiyar ba, wajen tallafawa ayyukan ginin hanyoyin mota da na jiragen kasa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China