in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birnin Fatakwal na Nigeria ya zama birnin litattafai na duniya
2014-04-24 14:12:38 cri

Ranar 23 ga watan Afrilu rana ce ta karanta litattafai ta duniya, a wannan rana kuma an nada birnin Fatakwal na jihar Rivers da ke kudancin kasar Nijeria 'birnin litattafai na duniya', sabo da haka ne Fatakwal ya zama birni na farko a yankunan da ke kudu da Sahara da ya samu wannan lambar yabo, wadda wa'adinta shekara guda ce.

A wannan rana kuma, birnin Fatakwal ya gudanar da bukukuwa bila adadin domin murnar wannan ranar karanta litattafai ta duniya. Bukukuwan sun hada da 'karanta litattafai tare da marubuta', da nune-nunen adabi da al'adun duniya, da taron kara wa juna sani, da wasannin kwaikwayo da dai sauransu. Daga cikinsu kuma, abin da ya fi samun karbuwa daga yara shi ne 'shahararrun mutane sun karanta shahararrun laittattafan adabi', masu shirya bikin sun gabatar da cewa, suna fatan wannan biki zai zubarar da sha'awar karanta litattafai ga yara.

Bisa labarin da muka samu, an ce, a cikin shekara guda mai zuwa, kasar Nigeria za ta gudanar da ayyuka da dama dangane da al'adu, domin yada bayanai kan adabin Afirka. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China