in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ba za ta amince da alakanta batun tsibirin Diaoyu da kawancen Amurka da Japan ba
2014-04-24 11:54:00 cri

Mahukuntan kasar Sin sun bayyana adawar su ga yunkurin da ake yi, na sanya batun ikon mallakar tsibirin nan na Diaoyu, karkashin kariyar kawance dake tsakanin Amurka da kasar Japan.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ne ya bayyana hakan, yayin taron manema labaru na rana-rana da ya gudana a ranar Labara. Mr. Qin ya ce, bai dace waccan dangantaka ta Amurka da Japan, ta kawo wa kasar Sin tarnaki, ga ikon mallakar yankunanta ba. Ya kuma yi kira ga Amurka da ta martaba alkawarinta, na kin goyon bayan wani bangare, a takaddamar da ake yi game da tsibirin na Diaoyu.

Wannan dai tsokaci na Mr. Qin ya zo ne bayan da shugaba Barack Obama na Amurka, ya bayyanawa wata jaridar kasar Japan cewa, kasarsa za ta yi adawa da duk wani kokari na yiwa Japan makarkashiya game da tsibirin na Diaoyu.

Kasar Japan dai ta taba mamaye wannan tsibiri da ake tababa a kansa a shekarar 1895, kafin dawowarsa karkashin ikon kasar Sin bayan yakin duniya na biyu, wanda kuma hakan ke kunshe, cikin kundin bayanan dokokin kasa da kasa da aka tabbatar da su. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China