in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Sin ta samu nasara wajen kare ikon mallakar ilmi
2014-04-23 16:46:46 cri

Ranar 26 ga watan Afrilu, ranar duniya ce ta kare ikon mallakar ilmi. A bana ne kuma za a gudanar da bikin kewayowar wannan rana karo na 14. A ran 22 ga wata, hukumomi da dama na kasar Sin, sun nuna cewa kasar Sin za ta kara kare ikon mallakar ilmi, ta kuma riga ta samu nasara a wannan fanni.

A wannan makon da muke ciki, kasar Sin ta gudanar da aikin yada bayanai, dangane da kare ikon mallakar ilmi a duk fadin kasar. Bisa labaran da muka samu, an ce, a 'yan shekarun baya, kasar Sin ta dauki matakai bi da bi, na kafa tsarin dokokin kare ikon mallakar ilmi, kuma za a fara yin amfani da dokar alamun kayayyaki da aka gyara daga ranar 1 ga watan Mayu na shekarar da muke ciki.

Tuni kuma aka kammala aikin yin gyare-gyare, kan ka'idoji da mafunonin da suke da nasaba da kare ikon mallakar litattafai, da kare manhajar na'urori masu aiki da kwakwalwa, da kare ikon watsa labaru a kan shafin intanet, da kare sababbin tsare-tsare da dai sauransu.

Darektan hukumar kare ikon mallakar ilmi ta kasar Sin Mista Shen Changyu ya fayyace cewa, a bara yawan ikon mallakar ilmin da aka yiwa rajista ya samu karuwa cikin sauri. Adadin wadanda aka yarda da su a duniya a karon farko ya wuce dubu 20.

'A daukacin shekara ta 2013, yawan ikon mallakar ilmi da aka nemi rajista a fannoni uku ya kai miliyan 2 da dubu 377, inda yawan ikon mallakar ilmi da aka ba da iznin amfani da su ya kai miliyan 1 da dubu 313, daga cikinsu kuma yawan ikon mallakar ilmi da aka nemi rajista a fannonin kirkire-kirkire ya kai dubu 825, karo na farko da wannan adadi ya wuce sulusin adadin ikon mallakar ilmin da aka nemi yin rajistar sa, wanda kuma ya karu da kashi 26.3 bisa dari, idan aka kwatanta shi da yawan wanda aka samu a makamancin lokacin a bara.

Yawan ikon mallakar ilmi da aka yi rajistar amfani da su a duk duniya ya wuce dubu 20, wannan ne kuma karo na farko da adadin ya wuce kashi 10 bisa dari na adadin yawansa wanda aka nemi rajistar sa a duk fadin duniya. Sakamakon haka kasar Sin ta kai matsayi na uku a tsarin yarjejeniyar hadin kai kan ikon mallakar ilmin kirkira. Yawan ikon mallakar ilmin da ko wadanne jama'a dubu 10 ke da su, ya karu daga kaso 3.23 a shekarar 2012 zuwa 4.02 a shekarar 2013, wato tun kafin lokacin da aka tsara, an riga an cimma burin da aka tanada a cikin shiri na 12, na shekaru 5 na raya kasar Sin.

A yayin da ake samun saurin karuwar yawan ikon mallakar ilmin da aka yiwa rajista, hukumomin da abin ya shafa na kasar Sin sun fi mai da hankali kan kara ingancin ikon mallakar ilmin.'

Sai dai a 'yan shekarun baya, yayin da wasu kamfanonin kasar Sin suke nuna kayayyakinsu a kasashen waje, su kan gamu da matsaloli, dangane da ikon mallakar ilmi, wasu kasashen su kan soki kasar Sin da cewa, ba ta daukar matakai masu nagarta, wajen kare ikon mallakar ilmi. Game da haka, darektan hukumar kare ikon mallakar ilmi ta kasar Sin Mista Shen Changyu yana ganin cewa, ba safai a kan samu irin wannan matsala ba. Ya ce, yayin da kamfanonin kasar Sin suke shiga kasuwannin duniya, da farko dai ya kamata su shirya sosai a fannin kare ikon mallakar ilminsu, wato su nemi ikon mallakar ilminsu a ketare, su kuma yi amfani da ka'idoji, don kare ikonsu da halastacciyar moriyarsu. Su kuma yi shirin tinkarar matsalolin dake da alaka da ikon mallakar ilmi.

'Wani dalilin mai matukar muhimmanci da ke haddasar rikici shi ne, kamfanonin kasar Sin ba su fahimci ka'idojin ikon mallakar ilmi sosai ba, ba su da kwarewar amfani da ka'idoji wajen kare ikonsu da halaltacciyar moriyarsu. Game da haka, hukumar kare ikon mallakar ilmi ta kasar Sin na daukar matakai wajen tinkarar wannan matsala. A sa'i daya kuma, muna ba da jagoranci ga kamfanoninmu, da sa kaimi gare su, don su iya kare ikon mallakar ilmi a kasashen waje, haka kuma mun kafa tsarin ba da taimako ga kamfanonin Sin wajen kare ikonsu, don share fage ga kamfanonin Sin don su habaka kasuwanni a kasashen ketare.' (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China