in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar duniya ta sa jama'ar kasar Sin kara mai da hankali ga kare muhalli
2014-04-22 18:22:40 cri


Yau Talata 22 ga watan Afirilu, rana ce da ake bukukuwan sake zagayowar ranar duniya karo na 45, wadda a bana MDD ta sanyawa taken 'birni mai launin kore'. A nata bangare, gwamnatin kasar Sin ta sanya wa wannan rana taken 'Tsimin albarkatun kasa, da sauya fasahar raya kasa, don kare muhallin halittu'.

A matsayinta na wani muhimmin biki na kare muhalli, 'ranar duniya' tana janyo hankalin karin jama'a ga batun muhallin a dukkanin fadin duniyar nan da muke rayuwa cikinta.

Game da haka ne cibiyar nazarin harkokin rayuwar al'umma ta kasar Sin ta kan shirya wani biki a wannan rana, domin masana su rika sanya ido kan matsalolin da suka shafi muhalli. A wajen bikin da aka gudanar a wannan karo, Han Meng, wani masanin tattalin arziki, na ganin cewa, tsarin kare muhalli na kasar Sin ba shi da inganci, abin da ya sa ake samun matsaloli a wannan fanni sosai. Han ya ce,

'Da farko, kokarin habaka masana'antu, da raya birane ya sa ana kara amfani da makamashi tare da gurbata muhlli. Na biyu kuma, ana fama da rashin daidaito tsakanin yadda ake samar da makamashi, da ma'adinai, da hakikanin bukatun da ake da su. Na uku, ba a cika kokarin kare muhallin halittu ba. Sa'an nan na hudu, ana fitar da abubuwa masu yawa dake haifar da gurbatar yanayi, ba tare da kulawa da su yadda ya kamata ba. Na biyar, ana samun gibi sosai tsakanin yadda ake cin moriyar albarukatun kasa da yadda ake kokarin kiyaye muhalli.'

Hakika dai, jama'ar kasar suna da wayewa kan yadda gurbacewar muhalli take shafar zaman rayuwasu, musamman ma kan wani hazo mai gurbata muhalli da a kan gamu da shi a 'yan shekarun nan. Wasu na ganin wannan hazo na haifar musu da kaikayi a makogwaro, don haka sukan sanya makarin hanci da baki, da amfani da na'aurar tace iska a gida. Wasu kuma da kan fita waje don motsa jiki, yanzu su na rage lokacin fitowa don magance shakar gurbatacciyar iska.

Gaskiya yadda MDD ta saka ma bikin 'ranar duniya' taken ' birni mai launin kore' na da ma'ana, domin batun kare muhalli yana da alaka sosai da fasahar kula da birane. Alal misali, batun nan na kula da gurbacewar yanayi a birnin Beijing da yankin dake kewayensa, ya shafi rage amfani da kwal a matsayin makamashi, da takaita amfani da motoci, da rage fid da kura mai gurbata muhalli, fannonin da suke bukatar hadin gwiwa tsakanin masu lura da tsarin birane, da sashin kula da hanyoyin sufurin al'umma, da dai sauran sassa daban daban.

A wajen bikin da aka gudanar a wannan karo, wata kwararriya a fannin daidaita muhalli mai suna Xia Muchen, ta yi bayani kan yadda hukuma take iya daukar wasu matakai, don taimakawa kokarin da ake yi na rage fitar da iska mai gurbata muhalli. ta ce,

'Ga misali, kasar Jamus ta bukaci a lika tambura masu launuka daban daban kan tagogin motoci, bisa yawan hayaki mai gurbata muhalli da motocin suke fitarwa, sa'an nan an karkasa birane zuwa ungwanni daban daban, tare da sanya musu alamun cewa motoci masu tamburan wadanne launuka ne za su iya shiga ciki. Ban da haka kuma, a birnin London na kasar Birtaniya, an ba da fifiko ga kokarin raya tsarin kafafen sufuri na al'umma. Kaza lika tun taga shekarar 2003, hukumar birnin London ta fara karbar karin kudi kan motocin da suke shiga cibiyar birnin don rage cunkoson motacin, tare da tallafawa tsarin hanyoyin sufuri na al'umma.

A birnin Rome kuma, an dauki mataki mai taken 'ranar Lahadi mai launin kore', inda aka hana fitowar motoci a ranar, in ban da motoci masu amfani da tsabtaccen makamashi, kamar su wutar lantarki da dai makamantansu.

Sa'an nan a bangaren kasar Japan kuwa, ta sanar da kafa wata doka a shekarar 2000, da ta haramta yin amfani da motocin da suke yawan fitar da hayaki mai gurbata, da ya kai ma'aunin PM 2.5 a cikin birnin Tokyo, fadar mulkin kasar.'

Sanin kowa ne, tsimin makamashi, da rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli sun kasance hanyoyi masu amfani a kokarin kyautata muhalli. Don haka, kasar Sin ta riga ta gabatar da ma'auni a fannonin yawan amfani da makamashi, da fitar da iska mai dumama yanayi, da dai sauransu, cikin shirin kasar na kokarin raya kasa. Kamar yadda Xu Shaoshi, darektan hukumar raya kasa da gyare-gyare ta kasar ya bayyana. A cewar sa gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da daukar wasu kwararan matakai na kare muhalli a daukacin sassan kasar. Xu ya ce,

'Za a rika yanke hukunci mai tsanani kan wadanda suka keta dokokin kare muhalli, da bayyana jerin sunayan kamfanonin da suka gaza yin cikakken amfani da makamashi yadda ya kamata, da ma su fitar da gurbatattun abubuwa ba bisa doka ba. Duk wani kamfani da ya aikata irin wannan laifi, za a gurfanar da mai shi gaban kotu. Sa'an nan za a kara kokarin sa ido kan yadda ake bin dokokin da suka shafi tsabtace iska, musamman ma a wasu yankunan da suke kewayen Beijing, Shanghai da Guangzhou.'

Masanan kasar Sin suna ganin cewa, idan an lalata muhalli, ba za a iya maido da shi yadda yake a da ba, don haka ya kamata ko wane birni ya yi kokarin ba da fifiko ga kokarin kare muhallin da muke zama a ciki. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China