Rahoton hukumar girgizar kasa ta Mexico ya sheda cewa, girgizar kasar da ta abku a karfe 9 da minti 27 a safiyar ranar 18 ga wata bisa agogon wurin, ta faru a wani yankin teku da ke da tazarar kilomita 40 a kudancin birnin Petatlan na jihar Guerrero.
Zuwa yanzu, an ce gidaje kimanin 100 suka lalace a jihar Guerreron inda bala'in ya abku, kana tasirin girgizar har ma ya shafi birnin Mexico City da jihar Veracruz, inda ta dan lalata wasu gidaje. Sai dai ba a sanar da ko akwai mutanen da suka samu rauni ko kuma rasa rayuka sakamakon bala'in ba tukuna. (Bello Wang)