in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zartas da wata sanarwa a gun shawarwari na bangarorin hudu da suka shafi bantun Ukraine da aka yi a birnin Geneva
2014-04-18 16:26:32 cri

Amurka da Rasha da Ukraine da kungiyar tarayyar kasashen Turai EU sun shirya shawarwari na bangarori hudu a ran 17 ga wata a birnin Geneva, inda suka zartas da wata sanarwa, mahalarta taron sun amince da daukar matakai don sassauta tashe-tashen hankula a kasar Ukraine.

Kasar Amurka ce ta gabatar da shawarar shirya taron a tsakanin bangarori hudu. Mahalarta taron sun hada da babban sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, da babbar wakiliyar kungiyar EU mai kula da manufofin diplomasiyya da tsaro Madam Catherine Ashton, da ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov, da mukaddashin ministan harkokin wajen Ukraine Andrii Deshchytsia. Bayan da suka shafe kwana guda suna taron, sun cimma wata sanarwa a karshe, inda aka bukaci Ukraine da Rasha su dauki matakai a lokaci guda, don sassauta tabartarewar halin da ake ciki a kasar Ukraine. Bayan shawarwarin da suka yi, babban sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, da babbar wakiliyar kungiyar EU mai kula da manufofin diplomasiyya da tsaro Madam Catherine Ashton sun shirya wani taron manema labaru cikin hadin gwiwa, inda suka gabatar da manyan abubuwan da aka tanada a cikin sanarwar. Babban sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce,

'Mun samu ra'ayi daya, wato tilas ne bangarori daban daban da abin ya shafa su daina nuna karfin tuwo, da kawo juna barazana, da harzuka jama'a. Haka kuma a kwance damarar dukkan kungiyoyin dakarun da aka kafa ba bisa doka ba. A janye jiki daga gine-ginen gwamnati da aka mamaye ba bisa doka ba, ya kamata a mayar da su ga hukumomin kasar. Bugu da kari kuma, a janye jiki daga dukkan tituna, da filaye, da birane da garurruwan da aka mamaye ba bisa doka ba.'

Abubuwan dake cikin sanarwar sun hada da maganar tura tawagar 'yan kallo ta kungiyar kula da harkokin tsaro da hadin kai ta kasashen Turai domin su taimakawa gwamnatin kasar Ukraine da hukumomin jihohinta wajen aiwatar da matakan da aka dauka na sassauta tashe-tashen hankula da ake ciki. Amurka da EU da Rasha sun yarda da ci gaba da nuna goyon baya ga aikin da tawagar zata gudanar, ya kamata a tafiyar da yunkurin yin gyare-gyare kan tsarin mulki na kasar Ukraine a fili da kuma jawo hankulan bangarorin da wannan rikici ya shafa, ciki har da kafa wata hukumar da kabilu daban daban zasu rika shawarwari tsakaninsu, da yin la'akari sosai kan ra'ayin jama'a kan abubuwan da suka fi maida hankali a kai da sauraron ra'ayoyinsu kan gyaren tsarin mulkin kasar. Ban da wannan kuma, taron Geneva, bai shafi batun ci gaba da sanya wa Rasha takunkumi ba.

A nata bangare madam Catherine Ashton ta yi fatan bangarorin da abin ya shafa za su aiwatar da abubuwan da suka tanada a cikin sanarwar. Ta ce,

'Kamar yadda ka fada yanzu, an yi shawarwari a yau ne cikin sahihiyar zuciya, inda muka tattauna cikin yakini kan matakan da za a dauka wajen sassauta tashe-tashen hankula a kasar Ukraine. Sassauta tabarbarewar halin da ake ciki a Ukraine ya zama wani abin gaggawa a gabanmu. Mun samu ra'ayi daya kan cikakkun matakai da za a dauka, wadanda za a aiwatar da su nan gaba ba da jimawa ba. Ko da yake yadda muka nuna sanarwar yanzu tana da muhimmanci, amma muna fatan za a ci gaba da aiwatar da ita, ta yadda za'a samu wani sakamako mai kyau a gaba.'

Bayan wannan zaman taro, bi da bi ne, ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov, da mukaddashin ministan harkokin wajen Ukraine Andrii Deshchytsia suka shirya tarurrukan manema labarunsu, inda suka gabatar da matsayinsu.

Lavrov ya ce, idan gwamnati mai ci da ta hau mulki ta hanyar juyin mulki tana cewa tana wakiltar moriyar dukkan jama'ar Ukraine, to, tilas ne ta nuna yakini, ta saurari ra'ayin jama'ar wurare daban daban, ta zauna tare da su su yi shawarwari da juna. Lavrov ya ci gaba da cewa, ko kadan Rasha ba ta son tura sojoji a kasar Ukraine, dake abokantaka da ita, kuma 'yan uwan juna ne. Sabo da yin hakan zai saba wa moriyar Rasha.

Mukaddashin ministan harkokin wajen Ukraine Andrii Deshchytsia ya nuna maraba tare da nuna dari-dari ga wannan sanarwar da bangarori hudu suka cimma, ya karfafa cewa, tilas ne a aiwatar da sanarwar a cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

Babban sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce,

'Aikin da muka gama a yau shi ne, mu tabbatar da wasu ka'idoji, da tabbatar da nauyin da ke bisa wuyanmu. Abubuwan da wannan sanarwa ta tanada sun bayyana kokarin da muke yi, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne a aiwatar da abubuwan dake cikin sanarwar yadda ya kamata.' (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China