Farashin hannun jarin Weibo ya kai darajar dallar Amurka 17, cikin rana ta farko, farashinsa ya karu da kashi 19.06 bisa dari, watau a karshen ranar 17, farashin hannun jarin Weibo ya karu zuwa dallar Amurka 20.24.
Ganin cewa a kwanan baya, yanayin bunkasuwar hannayen jari da suka shafi harkokin kimiyya da fasaha na kasar Amurka ya samu koma baya, kafofin watsa labarai na kasar Amurka na ganin cewa, bai dace da Weibo ya shiga kasuwar Amurka a halin yanzu ba, duk da haka, yadda Weibo zai gudanar da harkokinsa a kasuwar Amurka zai ci gaba da janyo hankulan jama'a. (Maryam)